An yi zanga-zangar goyon bayan Tinubu a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Masu zanga-zangar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun fito kan tituna a Jihar Kano.

Masu wannan zanga-zanga suna yin ta ne a daidai lokacin da Nijeriya ta ɗauki zafi da zanga-zangar nuna adawa da halin yunwa da tsadar rayuwa a ƙasar.

Masu wannan zanga-zanga sun fito ne ta titin Audu Baƙo da kuma Farm Centre suna bayyana adawa ga abin da suka kira zanga-zangar tashin hankali.

Sun kuma yi taro a Fadar Sarkin Kano da ke Nasarawa, inda suka saurari jawabai kan hanyoyin da za a magance matsalolin da ke addabar ƙasar.

Da yake musu jawabi, Abdullahi Muhammad Saleh ya ce, “Mun fito domin yaba ayyukan ci gaban da Shugaba Bola Tunubu ya aiwatar.

“Muna jinjina masa da ya kafa Hukumar Kula da Cigaban Arewa Maso Yamma, wadda za ta kawo kyakkyawan sauyi a yankin.

“Babbar hanyar bayyana rashin jin daɗi ita ce tattaunawa, ba fito-na-fito da gwamnati ba.

“Kowa na cikin wannan mummunan yanayi amma zanga-zanga ba ita ba ce mafita.

“Mu fara neman a zauna lafiya sannan mu haɗa kai wajen tattaunawa da gwamnati ba, don shawo kan matsalolin namu.

“Ba ma son marasa kishin ƙasa da ɓata-gari su ƙwace wannan zanga-zanga.

“Mu dai muna goyon bayan wannan gwamnati saboda mun san abubuwan da take yi.”

By ukarofi