Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon mataimaki ga Obasanjo, Okupe ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Dakta Doyin Okupe ya rasu.

A safiyar ranar Juma’a ne Dakta Okupe, mai shekaru 72 ya rasu, bayan fama da wani gajeren rashin lafiya da ake kyautata zaton cutar daji ce.

A shekarar 2022 ne aka naɗa shi a matsayin Darakta-Janar na jam’iyyar LP na zaɓen Shugaban ƙasa na 2023.

Daga bisani aka tilasta masa yin murabus sakamakon zarginsa da badaƙalar wasu kuɗaɗe.

By Babaji