‘Yan Nijeriya ne suka fi shan tsadar tikitin jirgi a Afirka, inji NCAA

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Ƙasa, NCAA, ta yi ƙorafi game da yadda wasu kamfanonin jiragen sama suke ƙin kula da fasinjoji ƴan Nijeriya tare da cewa sune suke biyan kuɗi mafi tsada a Afrika.

Daraktan yaɗa labarai na NCAA, Michael Achimugu ya bayyana hakan a yayin ganawa da hukumar gudanarwar Kamfanin RwandAir wanda ya ɗauki tsawon lokaci na mayar wa wasu fasinjojin Nijeriya kuɗaɗensu.

Ya koka gami da nuna rashin ƙwarewa da jami’an kamfanin suka nuna, wanda shi ya sabbaba jinkirin biyan fasinjojin kuɗaɗensu.

Rahotonni sun bayyana cewa kamfanin RwandAir na fama da matsalar rashin biyan fasinjoji kuɗaɗensu akan lokaci na tafiye-tafiyenda aka soke.

Kamfanonin jiragen sama na gida da na waje ana samun su da laifin rashin biyan fasinjojin da aka soke tafiyarsu akan lokaci kuɗaɗensu.

Achimugu ya bayyana cewa, fasinjojin Nijeriya sun cancanci a ba su kulawa sama da wadda suke samu saboda sun fi kowacce ƙasa a Afrika biyan kuɗin jirgi.

By Babaji