Majalisar Wakilai na shirin karɓe ikon gudanarwa da rajistar jam’iyyu a hannun INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Wakilai ta fara shirin karɓe iko daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na gudanarwa da yin rajista ga jam’iyyun siyasa a Nijeriya.

A ranar Alhamis ne ƙudirin da ke neman samar da hukuma ta musamman kan alhakin kula da gudanarwar jam’iyyu da ɗaukar nauyinsu ya tsallake karatu na biyu a majalisar.

Ƙudirin, wanda Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas da ɗan majalisa Markus Onobun daga Jihar Edo suka ɗauki nauyinsa, na neman a daina yin rajistar jam’iyyu da kula da su daga hannun INEC.

Haka kuma, ya na neman a samar da kwamitin shari’a na warware matsalolin rikici tsakanin jam’iyyu da mambobinsu.

Onobun ya ce, kira game da yin adalci ga hukumar zaɓe a Nijeriya na ɗaya daga cikin abinda al’umma ke yawan tattaunawa a ƴan shekarun nan la’akari da rikice-rikicen zaɓe da ake samu a kowane mataki na ƙasa.

Ya kuma ce, lallai ne sai an samu masu-ruwa-da-tsaki a siyasa suna yin abinda ya dace kafin a samu jagorori da shugabanci na gari.

Ɗan majalisar ya kuma ce mutane da dama suna ɗora wa INEC laifi a duk sadda aka samu wani rashin adalci a yayin zaɓuka.

Daga nan ne aka miƙa ƙudirin ga kwamitin lamuran zaɓe da harkokin siyasa na majalisar domin cigaba da nazari a kai.

By Babaji