Blueprint jigo ce a ɓangaren ingantattun labarai a Nijeriya – MD Haɗeja-Jama’are

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Manajan Darakta na Hukumar Kula da Kogunan Haɗeja da Jama’are, Riɓer Basin Deɓelopment Authority, Injiniya Bello Sani Gwarzo, ya bayyana kamfanin jaridun Blueprint a matsayin babbar jigo a ɓangaren ingantattun labarai da ya kamata hukumomi da ma’aikatun gwamnati su yi riƙo da su.

Ya bayyana hakan ne ya yin wata ziyara da tawagar jaridar Blueprint ta kai masa a ofishinsa da ke Hotoro, Kano.

Injiniya Bello ya ƙara da cewa, Hukumar Kogunan Hadeja da Jama’are  tana ayyukanta ne a Kano, Bauchi da Jigawa, to, amma ayyukanta duk Nijeriya ne.

Ya kuma ce duba da irin yadda suke gabatar da ayyukansu cikin gaskiya da riƙon amana ne ya sa gwamnatin taraya take ba su ayyuka daban-daban a wannan yanki, sannan idan gwamnati ta ba su miliyan ɗaya to ana ganin aiki miliyan ɗayan a ƙasa, hakan aikinsu ya karaɗe baki ɗaya.

“Ko a lokacin da aka shiga cikin matsin tattalin arziki gwamnatin tarayya ta ba mu kayan abinci tone na abinci mai yawa, kuma mun raba yadda ya kamata.

“Kwanan nan za mu raba injinan ban ruwa sama da 200 ga manoman rani a wannan yanki, za mu gayyato Blueprint.

“Sannan akwai ayyukan da za mu yi da ƙasar Masar da Morocco kan samar da eka na noma a wannan yanki,” inji Engr. Bello.

Malam Aminu Ado Ibrahim wanda shi ne Manajan daraktan kasuwanci da shiya-shirye na Jaridar Blueprint Newspapers ya bayyana cewa saboda muhimancin da Haɗeja Jama’are ta ke da shi ne ya sa ya tun daga Abuja kamfani ya turo shi zuwa Kano, domin gamsuwa da irin aikin da wannan hukumar ta ke yi musamman a kan aikin gona.

“Kuma duk wani aiki da za ku yi ko Press Release ko Press Conference Blueprint a shirye take a sanar da ita mu kuma za mu zo mu ɗauki rahoto.”

Sannan ya yi albishir da cewa Blueprint za ta riƙa kawo kwafin jarida a kowace rana kyauta, domin kyautata alaƙa da ke tsakani,” inji Mal. Aminu.

Ziyarar dai ta samu halartar Daraktoci na Haɗeja da Jama’are tare da ma’aikata na fannoni daban-daban.

By ukarofi