Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A shekarun baya ne gwamnatin Jihar Katsina ta rufe kasuwannin sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da ya janyo taɓarɓarewar tsaro a kasuwannin.
Wasu daga cikin aikace-aikacen kwamitin da sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari ya ƙaddamar sun haɗa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankunan Batsari da Sheme kan hanyoyin da za a bi wajen buɗe kasuwannin.
Haka kuma Faskari ya ce kwamitin zai gano wasu matsaloli da ka iya tasowa bayan buɗe kasuwannin da yadda za a magance su.
Da bada shawarwari da zai taimaka wa gwamnatin Katsina wajen tabbatar da samun nasarar buɗe kasuwannin.
Kwamishinan raya karkara da cigaban al’umma Farfesa Abdulhamid Ahmed shine shugaban kwamitin.
Sauran ‘yan kwamitin sun haɗa da Kwamishinonin tsaro da na Shari’a, akwai mai ba gwamna shawara kan cigaban kasuwanni da kuma shugabannin ƙananan hukumomin Batsari da Faskari.
Sauran sun haɗa da jami’an tsaro na ‘yan sanda, DSS da sauran su.
An ba Kwamitin nan da mako biyu ya miƙa rahoton sa.
