Gwamnati ta ware biliyan N4.8 don kula da masu fama da ƙanjamau a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ware naira biliyan 4.8 domin ci gaba da samar da Kula wa masu fama da cutar ƙanjamau a ƙasar nan

Gwamnati ta ware waɗannan kuɗaɗe domin ganin masu fama da cutar sun ci gaba da samun magungunan daƙile cutar a Nijeriya.

Ware kuɗaɗen na daga cikin matakan da gwamnati ta ɗaukan na miƙewa tsaye domin ɗaukan nauyin yaƙi da cutar ƙanjamau musamman yanzu da gwamnati Amurka ta rage yawan kuɗaɗen tallafin da kasan ke samu domin yaƙi da yaɗuwar cututtuka.

Bayan haka gwamnati ta kuma ware naira biliyan 1.07 domin inganta fannin kiwon lafiyar ƙasar nan.

Gwamnati ta yi hakan ne a ƙarƙashin shirin ta na ‘HOPE’ wanda ta ƙirƙiro domin samar da ci gaba da ababen more rayuwa wa mutane a Nijeriya.

Mutane da dama musamman jami’an lafiya sun yaba da hakan da gwamnati ta yi musamman yadda ware kudaden zai taimaka wa gwamnati wajen rage yawan dogaro da tallafin kasashen waje.

Jami’an lafiyan sun yi kira ga gwamnati da ta zage damtse wajen ware kuɗaɗen tare da mai da hankali domin tabbatar da kuɗaɗen an yi amfani da su ta hanyoyin da ya kamata.

By ukarofi