’Yan bindiga sanye da rigar jami’an EFCC sun sace baƙi a otel

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu ’yan bindiga da suka yi basaja a matsayin Jami’an Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon ƙasa Ta’annati (EFCC) sun yi garkuwa da mutane 10 a otel ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma ƙwararre kan yaƙi da tada ƙayar baya, Zagazola Makama, ya ruwaito majiyoyin leƙen asiri na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:58 na asubahin ranar Talata 27 ga watan Fabrairun 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki otel ɗin ne, inda suka yi ikirarin cewa jami’an hukumar EFCC ne a wani samame da jami’an suka kai.

“An tattaro cewa waɗanda ake zargin sun dakushe kyamarorin sa ido na CCTɓ na otel ɗin kafin su shiga ɗakunan baki ɗaya bayan ɗaya sannan suka kwashe mutane 10 da ƙarfi zuwa inda ba a sani ba,” inji rahoton.

A cewar rahoton, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na hukumar leƙen asiri ta jihar (Acpol SID), ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da gano waɗanda aka sace.

Makama ya ƙara da cewa, “An buƙaci jama’a da su sanya ido tare da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi, yayin da hukumomi ke ƙara ƙaimi wajen bankaɗo bayanan da suka shafi harin.”

By ukarofi