Ɗan wasan gaba na Real Madrid da Brazil, Vinicius Jr, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon maza na duniya a gasar FIFA Best Awards. Vinicius, mai shekaru 24, ya karɓi wannan lambar yabo ne a wani biki da aka gudanar a birnin Doha, Qatar.
Tun da farko, Vinicius da kulob ɗinsa sun ƙaurace wa bikin Ballon d’Or na baya-bayan nan bayan da ya sha ƙasa ga ɗan wasan Manchester City, Rodri. Sai dai wannan lambar yabo ta FIFA Best ta zo masa a matsayin gagarumar nasara, bayan rawar gani da ya taka a kakar wasa ta 2023-24, inda ya zura kwallaye 24 tare da bayar da taimakon kwallo 11 da suka taimaka wa Real Madrid lashe gasar zakarun Turai.
A yayin bikin, Aitana Bonmati, ‘yar wasan Barcelona, ta lashe kyautar gwarzon ‘yar kwallon ƙafa ta mata karo na biyu a jere, sakamakon bajintar da ta nuna a shekarar da ta gabata. Wannan nasara ta Bonmati na ƙara nuna irin tasirin da take da shi a duniyar ƙwallon ƙafa ta mata.
Wannan ne karo na farko da Vinicius Jr ya lashe wannan gagarumar lambar yabo ta FIFA best, bayan da Lionel Messi ya lashe ta a lokuta biyu na baya, sai Robert Lewandowski wanda ya lashe a shekarun da suka gabata. Wannan nasara ta zama wani babban tarihi a rayuwar ɗan wasan bayan ƙauracewarsa ga bikin Ballon d’Or a watan Oktoba.
