
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar ta amince da kasafin kudin ne a zaman majalisar, ƙarƙashin Jagorancin Kakakinta, Hon. Nasir Yahaya wanda adadinsa Naira biliyan 692 da Gwamnan Jihar, Dikko Raɗɗa
ya gabatar.
Amincewa da kasafin kuɗin na 2025 ya biyo bayan karanta rahoton kare shi ne da shugaban kwamitin, Hon. Lawal H. Yaro Away ya gabatar ya kuma karanta.
Yayin tattauna batun, majalisar ta yaba wa gwamnan inda ta ce a tarihi ba a taɓa kasafin kudi irin wannan ba, wanda aka bai wa manyan ayyuka kaso mai tsoka da za su taɓa rayukan talakawa kai tsaye.
Ƙudirin farko shi ne dokar shirin bunƙasa ci-gaban al’umma inda daga nan ne majalisar ta tura wa kwamitin kula da walwalar Jama’a da na kula da ayyukan kantanan hukumomi, domin bada shawarwari.
Haka kuma majalisar ta yi karatu na biyu ga dokar ƙirƙiro hukumar kula da samar da wutar lantarki, sai ta bai wa kwamitin kula da makamashi domin bada shawarwari.
Na uku, Majalisar ta yi karatu na biyu ga ƙudirin dokar ƙirƙiro hukumar kula da inganta harkar noman rani, sannan ta miƙa wa kwamitin aikin gona da na albarkatun ruwa domin bada shawarwari.
Sai ƙudirin dokar ƙirƙiro hukumar dake bada kariya ga harkokin saka hannu jari a Jihar wanda shi ma ta miƙa wa kwamitin dake da alhakin kula da wannan ɓangaren domin bada shawarwari.
