Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Marubuta mata na onlayin masu rubutu da harsunan Hausa da Turanci sun kafa wata sabuwar ƙungiya da suka sanya wa suna Women of Words, a turance, da nufin haɗa kan ɗaukacin mata masu rubutun adabi, don faɗakar da al’ummar Arewa.
Kungiyar wacce a yanzu haka ta kammala bin dukkan matakan da suka dace na rijista, ta zama halastacciyar ƙungiya, tare da fara ɗaukar sabbin mambobi daga sassan Nijeriya ba ma a Arewa kaɗai ba. Kuma a halin yanzu har ta samar da shugabannin riƙo da za su riƙa kula da harkokin gudanar da ƙungiyar, da suka haɗa da Hassana Suleiman Isma’il da aka fi sani da Sanah S. Matazu a matsayin shugaba, sai Sakina Yazid da take a matsayin Mataimakiyar Shugaba, da Rufaida Umar Ibrahim da aka bata matsayin Sakatariya.
Kungiyar wacce ta fara da mambobi biyu kacal, wato Sanah da Rufaida, kafin shigar Sakina da Lubna, yanzu tana da adadin mambobi da suka kai kimanin 25, waɗanda kuma da suka fito daga ƙungiyoyin marubuta daban-daban. Ya zuwa yanzu dai tuni waɗannan sabbin mambobi sun yi rijista kamar yadda sharaɗin shiga ƙungiyar yake.
Dalilin kafa wannan ƙungiya, a cewar shugaba Hassana Suleiman shi ne, wayar da kan marubuta mata, da samar musu ‘yanci a duniyar rubutu. Inganta tsarin rubuce-rubucensu da bunƙasa rayuwar marubuta mata ta fannin samar da damar ƙarin ilimi da horarwa a fage daban-daban. Da kuma buɗe hanyoyin da za su kawo duk wani abu na cigaba a harkar rubutu.
Ta ce, “Muna fatan mambobin wannan ƙungiya su zama daban da sauran marubuta, kuma a ga sauyi a tsarin rubutunsu ta hanyoyin da aka saba gani a baya, don a kawo gyara a harkar rubutun adabi da ake yi cikin harsunan Hausa da Turanci, a nan yankin Arewa. A ganina, idan muka ɗauki salon baya tamkar mun sake maimaita abin da ya wuce ne, kuma hakan yana ƙara mayar da mu baya ne, yayin da ‘yan uwanmu da ke Kudu suke ta samun cigaba, da samun damar shiga manyan gasanni na Afirka da duniya bakiɗaya.”
Ta cigaba da cewa, “Muna son kawo sauyi a harkar rubutu sosai ta fuskar zamani da kuma sauye-sauyen da zamani kansa ya kawo mana. Rubutun marubutan ƙungiya ba zai tsaya iya rubutun labarai kaɗai ba, zai shafi duk wani abu da ya ci sunan rubutu kuma ya kamata a rubuta shi. Kama daga kan abin da ya shafi sana’o’i, kasuwanci, siyasa, kimiyya da fasaha, girke-girke, har ma da abin da ya shafi nazarce-nazarce na ilimi a ɓangarori daban-daban.”
Ita ma mataimakiyarta, Sakina Yazid, nuni ta yi da cewa, “Akwai ƙungiyoyin marubuta mata da dama musamman ma na onlayin, sai dai mafi yawancin su manufofinsu ba su dace da namu ba. Sannan kuma yawancin ƙungiyoyin na marubuta labari ne da harshen Hausa kawai. Mu kuma muna so ne ya kasance duk wata marubuciya ba kawai ta labaran hikayoyi ba har ma da duk wani littafin za ta rubuta a kowanne fanni na ilimi. Sannan kuma ba lallai rubutun ya kasance da Hausa ba, za mu haɗa kai da sauran marubutan turanci na Arewa. Muna ganin wannan shi ne tsarin da zai kawo mana cigaba kuma ya wayar da mu ta fuskar zamani.’
Mataimakiyar shugaban ta kuma ƙara da cewa, muna son mu ga marubuta mata suna cin moriyar rubutunsu, ta fuskar samun kuɗaɗe. Sannan kuma za su amfana ta hanyar shigowa wannan ƙungiya wajen samun ilimin dabarun rubutu da kuma yadda ake kasuwancinsu a zamanance. Muna ganin wannan zai samu ne ta hanyar samar da wata gayya ta jama’a, da a turance zan iya cewa da ‘community’ na marubuta mata ‘yan Arewa.’
Wani abin ƙayatarwa game da wannan ƙungiya shi ne yadda shugabannin suka yi kyakkyawan tunani wajen yi mata tsari na ilimantarwa, inda suke nuna cewa, shiga wannan ƙungiya ga marubuciya kamar shiga makaranta ne, domin kuwa akwai damarmaki da dama da za su taimaketa ta ƙara bunƙasa rubutunta.
A ɓangaren alaƙar ƙungiyar da sauran mata marubuta masu talifi da ba sa rubutu a onlayin, ko kuma ba sa bai wa rubutu a onlayin ɗin ƙarfi sosai, ƙungiyar ta ce tana maraba da su. A cewar Sakina, wannan ƙungiya ba wai ta mata masu rubutu a onlayin kaɗai ba ce, ƙungiya ce da mata masu yin rubutu a kowanne tsari za su iya zama mambobi a ciki.
Kodayake marubuta mata sun taɓa kafa wata ƙungiya makamanciyar wannan a shekarun baya, wacce aka kira da Mace Mutum, amma a yanzu ba ta tasiri kamar da. Marubutan sabuwar ƙungiyar WoW, suna ganin sun tanadi wasu ƙa’idoji da tsare-tsare da za su hana ta rushewa a nan gaba.
Sanah Suleiman ta ce, “Mun kafa ƙungiyar mu ne ba a kan ra’ayin wani mutum ɗaya ba, mun yi tanadin yadda a duk lokacin da mutum ya ji ba ya so ya cigaba da kasancewa mamba zai iya ficewa ya bar ƙungiya, kuma ayyuka su cigaba da gudana. Ko da kuwa matsala ce ta shugabanci.”
Kodayake, ƙungiyar ba kamar sauran ƙungiyoyin marubuta take ba, wanda ake sanya mutum kyauta ko kuma a biya wasu kuɗaɗe ýan ƙalilan, Women of Words ta tanadi cewa, kowacce marubuciya sai ta biya wasu kuɗaɗe, a matsayin rijista, don ta samu damar amfana da duk wasu tanade-tanade ko abubuwan moriya da ƙungiyar ta samu. Kamar yadda tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada
