Dalibai miliyan 1.38 sun amfana da rancen karatu – NELFUND

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Asusun Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND), ya bayyana cewa aƙalla ɗalibai 1,388,592 sun riga sun amfana da shirin lamunin karatu da gwamnati ta ƙaddamar.

Rahoton yau da kullum da asusun ya fitar ranar Litinin ya nuna cewa tun bayan fara shirin, an karɓi jimillar buƙƙatun lamuni 1,778,854 daga ɗalibai a faɗin ƙasar. An kuma samu ƙarin buƙatu guda 353 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata, yayin da kaso na ƙaruwa ya tsaya a matakin kashi 0.0.

Dangane da kuɗaɗen da aka fitar, NELFUND ya bayyana cewa zuwa ranar 2 ga Afrilu, 2026, an biya kuɗaɗen makaranta ga cibiyoyi 288 da suka ci gajiyar shirin, inda jimillar kuɗin da aka biya ta kai N157,455,283,093.25.

Haka kuma, an ware kuɗi har N84,945,632,200.00 a matsayin alawus-alawus na kula da ɗalibai na yau da kullum, wanda hakan ya kai jimillar kuɗin lamunin da aka rarraba zuwa N242,400,915,093.25.

An ƙaddamar da wannan shiri ne bisa dokar bayar da lamunin karatu mai taken Lamunin ɗalibai (Access to Higher Education) Act, 2024, wadda Bola Ahmed Tinubu, Shugaban ƙasa, ya sanya wa hannu. Shirin lamunin na NELFUND ba ya ɗauke da riba, kuma yana bai wa ɗalibai damar biyan kuɗin makaranta tare da samun tallafin rayuwa na wata-wata.

A cewar tsarin shirin, za a fara biyan bashin ne bayan shekaru biyu da kammala hidimar ƙasa ta NYSC, domin bai wa masu cin gajiyar damar samun daidaito a rayuwarsu kafin fara biyan bashin.

Shirin na NELFUND na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin tarayya na ƙoƙarin sauƙaƙa wa matasa samun ilimi mai zurfi, tare da rage matsin tattalin arziki da ke hana wasu ci gaba da karatu.

Duk da haka, masana na ganin cewa ɗorewar shirin zai dogara ne kan yadda za a tabbatar da gaskiya da kuma tsari mai kyau wajen dawo da kuɗaɗen, domin tabbatar da cewa shirin zai ci gaba da anfani ga al’ummomi masu zuwa.

By ukarofi