Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata mace mai suna Mallama ta haifi jarirai maza tagwaye a yayin wani taron tallafa wa mata da aka gudanar a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Rahotanni sun nuna cewa taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, tare da mai ɗakinsa Hajiya Zainab Nasare, inda dubban mata suka taru domin samun tallafin kuɗi don bunƙasa sana’o’insu.
An shirya taron ne ƙarƙashin wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna “Mu gudu tare, mu tsira tare”, inda aka gudanar da shi a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.
A lokacin da ake tsaka da shirin, sai mace Mallama ta shiga naƙuda, inda nan take ta haifi jarirai biyu maza, lamarin da ya ja hankalin mahalarta taron.
Bayan sanar da haihuwar, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Suru/Bagudo, Bello Dallatun Ka’oje, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan biyar domin kula da lafiyar uwar da kuma shirye-shiryen suna.
An kuma tabbatar da cewa an garzaya da uwar da jariran nata zuwa asibiti domin samun cikakken kulawar likitoci.
A wani ɓangare na tallafin, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi, Faruk Aliyu Yaro Enabo, ya bayar da zanen gado guda miliyan ɗaya domin rabawa mambobin ƙungiyar, a wani mataki na murnar Sallah Babba.
Haka kuma, ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 30 ga matan tare da ba shugabannin ƙungiyar mota.
Da yake jawabi a wurin, Enabo ya jaddada muhimmancin mata a fannoni daban-daban na rayuwa, musamman siyasa da kasuwanci, inda ya bayyana su a matsayin ginshiƙin samun nasarar zaɓe, yana mai alƙawarin ci gaba da inganta rayuwar mata kamar yadda gwamnan jihar ke yi.
Lamarin haihuwar tagwayen ya ƙara haskaka muhimmancin irin waɗannan shirye-shiryen tallafa wa mata, musamman wajen inganta jin daɗinsu da kuma samar musu da dama a rayuwa.
