Dalilan da suka sa ƙauyukan Sin samun ci gaba

Daga BELLO WANG

Wasu abokaina ‘yan Najeriya, wadanda suka taba zama a ƙasar Sin, su kan ambaci yadda zaman rayuwa a cikin biranen Sin ya burge su, yayin da muke hira. Sai dai na kan tunatar da su cewa, ba abun mamaki ba ne, ganin irin saurin ci gaba da aka samu a kauyukan ƙasar Sin.

Kauyena yana lardin Anhui dake gabashin ƙasar Sin, wani wuri ne dake cikin duwatsu. Yayin da nake ƙarami, ba na son komawa kauyen tare da iyayena, saboda hanyar ba ta da kyau: a kan kwashe sa’o’i 10 a cikin jirgin kasa, sa’an nan a ci gaba da hawa tarakta har tsawon awa ɗaya. Ban da wannan kuma, bayan gidan da mutanen ƙauyen suke amfani da shi ba shi tsabta, hakan yana tsorata ni.

Sai dai zuwa yanzu, ƙauyen ba kamar yadda yake a baya ba. Jirgin ƙasa mai saurin gudu ya samar da sauƙi sosai ga mutanen da suke neman komawa ƙauyen. Kana mutanen wurin sun gina manyan benaye, ga kuma muhalli mai tsabta da kayatarwa. Ban da haka kuma sun fara yin amfani da dakunan dake cikin gidajensu wajen karɓar baki masu yawon shakatawa.

To, me ya sa ake samun ci gaba sosai a ƙauyukan ƙasar Sin, cikin gomman shekaru da suka wuce?

Dalili na farko, a ganina, shi ne niyyar gwamnati ta raya ƙauyuka, da yadda take ƙoƙarin aiwatar da niyyar.

Babbar manufar jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin dake kan karagar mulki a ƙasar, ita ce ƙoƙarin kyautata zaman rayuwar jama’a. Saboda haka gwamnatin ƙasar ba za ta taba barin ragowar sassan ƙasar, ko kuma wasu mutane a baya ba, yayin da take ƙoƙarin raya tattalin arzikin ƙasar.

Hakan ya sa gwamnati ta fito da dimbin manufofi wajen raya ƙauyuka, da kyautata zaman rayuwar manoma. Misali taimakawa ƙauyuka wajen janyo jari, da samarwa manoma fasahohin zamani na aikin gona, da samar da rance don raya aikin yawon shakatawa a yankin karkara, da dai sauransu.

Dalili na biyu, shi ne yadda wasu matasan ƙauyuka suka komawa gida, bayan da suka samu ilimi, don taimakawa wajen raya ƙauyukansu. A cikin ƙauyukan da na ziyarta a shekarun baya, na kan ga wasu matasan da suka kammala karatun jami’a a cikin manyan birane, inda suka shafe wasu shekaru suna aiki a can, daga bisani sun koma kauyukansu, sun fara aiki a matsayin jami’ai.

Yadda aka wayar musu da kai, ya samar musu da damammakin raya wasu sana’o’i da suka dace da yanayin ƙauyukan, kana sun fahimci muhimmancin yin amfani da manufofin da gwamnati ta tsara na raya yankunan karkara.

Ban da wannan kuma, dalili na uku shi ne al’adun Sinawa na jure wahalhalu da ƙoƙarin aiki. A kauyukan da na je, na ga wasu tsoffi da yawa da suke gudanar da ayyuka daban daban, misali sayar da kaya, ko kuma nuna fasahohin hannu, har ma wasunsu na tuka manyan motocin tsabtace muhalli.

Haka ma dattawa na ƙoƙarin aiki, balle ma matasa. Sinawa suna ɗaukar ƙoƙarin aiki a matsayin wata muhimmiyar ɗa’a. Kana nagartattun manufofin gwamnati su ma sun sa mutanen ƙasar ke da wani tunani na ƙoƙarin aiki da samar da hidimomi, don kyautata rayuwarsu, gami da ba da gudunmowa ga ci gaban ƙasa.

A cikin ƙauyukan ƙasar Sin, ana iya ganin yadda mazauna suke da imanin cewar, za su ƙara jin dadin zaman rayuwarsu a nan gaba. Wannan imani ya tabbatar da cewa, ba za a taba daina ƙoƙarin raya ƙauyukan ƙasar, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wuraren ba.