Yajin Aiki: Rassan ASUU na kaɗa ƙuri’a don ɗaukar matakin ƙarshe

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na neman cimma matsaya dangane da yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), rassan ƙungiyar na kaɗa ƙuri’a a tsakaninsu.

Majiya mai ƙarfi daga shugabancin ASUU ta ce, za a kaɗa ƙuri’ar ne tsakanin Talata da Laraba.

A cewar majiyar, bayan kaɗa ƙuri’a za a tattara sakamakon a miƙa wa uwar ƙungiya don ɗaukar makin ƙarshe.

“Mun samu umarnin haka ne bayan tattaunawar da muka yi da Shugaban Majalisar Wakilai a ranar Litinin. Shugaban Majalisar ya shigo a daidai lokacin da ake da buƙatar haka.

“Rassan ƙungiyar za su kaɗa ƙuri’a tsakanin yau (jiya Talata) da gobe (yau Laraba) wanda bayan haka za a tatta sakamakon a miƙa wa uwar ƙungiya,” inji majiyar.