Daga SAIDU AHMAD DUKAWA (Phd)
Ga dalilai guda tara (9) daga cikin dadlilan da suka janyo kiki-kaka tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU).
Zan saka su a sigar mahawara domin sauƙin fahimta ga mai karantawa. Da fatan wannan gudunmawar za ta taimaka wajen lalubo bakin zaren ta yadda za a magance matsalar.
- Gwamnati: Ba za mu cire ku daga tsarin IPPIS ba, saboda tun daga ranar da muka fara amfani da shi muke samun rarar kuɗi daga abinda muke biya na albashi.
ASUU: Ba duka rarar da kuke gani ce ta samu daga toshe kofar zurarewar kuɗi ba; IPPIS ta yankewa duk wani ma’aikacin jami’a [babba da ƙarami] albashinsa; misali: Babban Malami (Senior Lecturer) yana rasa naira dubu arba’in (N40,000) duk wata [na yi misali da matakin da nake ne, saboda yaƙini da nake da shi];
Kun yi mana alƙawarin za ku gyara irin wannan kuskuren, idan muka koma daga wancan yajin aikin, amman kimanin shekara biyu da komawarmu, har yau ba ku gyara ba; kuma babu tabbas yanzu ma idan muka amince muka koma idan ba za ku kwata karya alƙawari ba.
- Gwamnati: To yanzu ku je mun yi muku ƙarin albashi. Daga yanzu duk babban malami yana da karin Naira dubu talatin (N30,000). Amman ku janye yajin aikin. [wannan yana nufin mai rasa 40,000 za a dawo masa da 30,000; rashin ya ragu zuwa 10,000; amman da iyalinsa da Duniya za su ɗauka an yi masa ƙarin albashi].
ASUU: A’a, ku riƙe ƙarinku. Ku cika mana alƙawarin da kuka yi mana a baya, kamar haka:
a) Ku daina yankar mana albashi da sunan IPPIS;
b) Ku dawo mana da kuɗin da kuka yanka tun daga lokacin da kuka saka mu a IPPIS; sannan
c) Ku yarda mu zauna mu yi yarjajjeniya game da abinda ya kamata a qara mana a tsari na babu cuta, ba cutarwa.
- Gwamnati:To ai kuɗin da kuke nema sun yi yawa, gwamnati ba ta da shi a yanzu.
ASUU: to ai rabi haƙƙi ne na waɗanda muke wakilta, kuma ba su ce sun yafe ba. Ku ne kuka yankar musu babu gaira babu dalili. Kuka qi dawo da wanda kuka yanka, kuka cigaba da yanka, har kuɗin ya taru. Rabi kuma alƙawari ne kuka ɗauka domin gyara jami’o’in da inganta yanayin koyo da koyarwa. Idan kuka hana, jami’o’in za su durƙushe.
- Gwamnati: To ai idan an bayar da kuɗin inganta jami’o’in, rashawa ake tafkawa, sai a ga kamar ba a bayar ba!
ASUU:
a) Mu dai a biya mambobinmu haƙƙoƙinsu;
b) Ragowar kuɗi kuma ku bai wa wakilanku (Shugabanni da jagororin jami’o’in); alabarshi,
c) Duk wanda kuka kama ya tafka rashawa ku hukunta shi, za mu goyi bayanku.
- Gwamnati: To ai yanzu ba ma kwa iya yin wani binciken a zo a gani, ga laifuffuka kala-kala da kuke tafkawa, ga shegen taurin kai!!!
ASUU: a) Ai yana daga cikin dalilin da ya sa muka yi yarjajjeniya da ku cewa duk shekara biyar za ku riƙa naɗa “Visitation Panel” (wani kwamiti mai ƙarfi wanda yake wakiltar Shugaban Ƙasa a Jami’ar Tarayya, ko Gwamna a Jami’ar Jiha) domin ya ziyarci kowace jami’a, ya aiwatar da binciken ƙwaƙwaf, ya bai wa gwamnati shawara a kan matakan gyara. Amman sai ku ki naɗa kwamitin har sai mun yi muku yajin aiki. A yanzu haka kwamitin ƙarshe da kuka naɗa har yanzu ba ku fitar da shawarwarinsa ba ballanta ku aiwatar.
b) Binciken ilimi kuwa muna yin iya abinda yanayi ya bamu damar yi. Mu ma alfaharinmu ne mu yi fiye da haka, amman yanayin ya yi ƙunci; shi ya sa muke so ku inganta yanayin ko ma yi fiye da abinda muke yi; amman
c) Taurin kai kuwa, na neman ku fahimce mu ne, ko a gudu tare a tsira tare.
- Gwamnati: Duk maganar nan da ake yi don ba kwa son IPPIS ne, saboda ta toshe muku kafar zuwa jami’o’i da yawa kuna koyarwa; ba kwa tara hankalinku wuri guda, kuna cutar da ɗalibanku.
ASUU: gyara wannan matsalar shi ya fi komai sauƙi:
a) Ku daina buɗe jami’o’i barkatai; ku daina bai wa ‘Yan kasuwa lasisin buɗe jami’o’i barkatai; sai a samu sauƙin zawarcin Malamai daga tsofaffin jami’o’i; kuma masu haɗamar cikinmu su rasa kasuwa;
b) Ku inganta mana albashinmu, sai ya rage matsin da yake tura wasu neman wurin da za su je koyarwa; sannan;
c) Ku inganta tsofaffin jami’o’in ta hanyoyin da muka baku shawara, sai su ƙara yawan ɗaliban da suke ɗauka. A yanzu tsofaffin jami’o’i ba sa iya ɗaukar fiye da abinda suke ɗauka saboda kun gagara inganta yanyinsu; wannan ta sa ake samun ƙarancin gurbi ga masu buƙatar shiga jami’a; ku kuma sai kuke gwammacewa ku buɗe sababbin jami’o’i ba tare da la’akari da a ina za a samo malaman da suka dace ba.
- Gwamnati: To, a matsayinku na masu ilimi, ku yi tunanin yadda jami’o’i za su iya riƙe kansu da kansu mana, a madadin dogaro da gwamnati!
ASUU: Mu ma muna son hakan; amma dole sai gwamnati ta samar da yanayi mai kyau na yin hakan tukunna. Alal-misali, jami’a nawa ce take da “Dam” [matattarar ruwa] a ƙasar nan, har wacce take ta koyon aikin noma ce? Alhali aikin noma kaɗai zai iya rike kowace irin jami’a!
8.Gwamnati: To ba sai ɗalibai su riƙa biyan kuɗi fiye da wanda suke biya a yanzu ba!
ASUU: An zo wurin!!! Watau so ake ace wanda duk ba zai iya biya wa ɗansa maƙudan kuɗi ba ya hakura da tura ɗansa jami’a, komai basira da hazaƙa da Allah ya bai wa ɗan? Watau karatun jami’a ba na ɗan Talaka ba ne? To muna yi muku nasiha da cewar wannan halayyar, ta mayar da ilimi kasuwanci, ba za ta haifar wa da ƙasar ɗa mai ido ba.
Ƙasahen da ake buga misali da su cewar ɗalibai ne suke rage wa gwamnati nauyin kuɗin karatu suna da tsari na tallafi da kuma na rance, kuma tsarin ba ya karyewa. Mu kuwa kun karya tsarin bayar da tallafi sannan ba ku samar da tsarin rance ba.
Mu da muke tare da ɗaliban mun san jibin goshin da wasu suke yarfewa kafin su iya biyan kuɗin da kuke rainawa a yanzu. Muna jan hankalinku cewar idan kuka ce talaka ya fitar da rai daga muhimmin al’amari irin ilimi, to kuna gina wa ƙasar mummunan ramin mugunta!
- Gwamnati:To sai ku je da taurin kanku, ku cigaba da yaijin aikin, mu dai ba za mu biya mutum albashi ba matuƙar yana yajin aiki; domin akwai doka da ta hana biyan mai yin yajin aiki albashi; mu kuma ba za sabawa doka ba, don ku ji da kyau, ehe!!!
ASUU: Mantawa kuka yi, ai an tsara albashin Malamin jami’a bisa sharaɗin zai riqa gudanar da ayyuka kashi uku, kamar haka:
a) Binciken ilimi: wannan ya haɗa da duk wani karatu da Malami zai yi, tun daga karatun jarida zuwa na mujalla, da na yanar-gizo, har zuwa littattafai, domin inganta koyarwa;
b) Koyarwa: wannan ya haɗa da dirasa a cikin aji, da tsara jarrabawa, da gudanar da jarrabawa, da duba takardun jarrabawa da kuma fitar da sakamakon jarrabawa; sai
c) Hidima ga al’umma: wannan kuma ya kasu kaso biyu:
i. Hidima a cikin jami’a, wanda ya haɗar da ɗaukar nauyin gudanarwa, kamar kasancewa shugaban sashe (HOD), shugaban Tsangaya (Dean), Shugaban Cibiya (Darakta); da kuma
Kasancewa cikin kwamitocin gudanarwa: duk wani al’amari na jami’a yana da kwamitin kula da shi; da abinda ya shafi ɗalibai, da wanda ya shafi Malamai, da wanda ya shafi sauran ma’aikata, da wanda ya shafi kadarorin jami’a, da na tsaro, da na kiwan lafiya, da na binciken ilimi, da komai da kamai;
ii. Hidima ga al’umar gari: wannan ya hadar da amsa gayyatar lacca ga ƙungiyoyin al’umma, da amsa tambayoyi da fatawoyin ‘yan Jarida, da gudanar da shirye-shirye na musamman a kafafan yaɗa labarai; da rubuce-rubuce masu alfanu ga al’umma ko a jaridu, ko mujallu, ko kafafan sada zumunta na zamani, da makamantansu.
To tambayar a nan ita ce: wanne ɓangaren albashin za ku riƙe? Wace shaida kuke da ita cewa Malamai sun gudanar da yajin aikin a fannin binciken ilimi da hidimta wa al’umma?
Yajin aikinmu a fannin koyarwa ne kuma muna sane da cewa hutun jaki da kaya aka ne, saboda sai mun biya duk wani kwantan aiki da yake kanmu. Sabanin haka zai bayu ga ba za mu yi aikin da ba a biya mu ba.
Don haka, duk wani kwantai na aiki sai dai a nemo wasu, su yi shi, a biya su. Kuma wannan yana nufin babu wanda zai fita daga jami’a a yanzu, sannan babu wanda zai gusa daga ajin da yake zuwa aji na gaba!
Kammakawa:
Tirkashi! Mai karatu, ka ji wannan tirka-tirkar. Kai me ka fahimta daga wannan tsaka-mai-wuyar? Sannan wace shawara za ka bayar domin a fitar da jaki daga duma kuma a fitar da A’i daga rogo?
Allah Ta’ala ya ba mu mafita kyakkyawa.
Dr. Saidu Ahmad Dukawa Malamin jami’a ne, sannan Shugaba Sashen Nazarin gudanar da mulki na Jami’ar Bayero ta Kano.
