Dalilan dawowar Boko Haram – Badaru

Spread the love

Ministan tsaro na Ƙasa, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sake dawowar hare-haren Boko Haram a Jihar Borno wani ɓangare ne na shirin ƙungiyar na tayar da hankula a yankin Sahel, wanda hakan ya shafi ƙasashe kamar Najeriya, Mali, Burkina Faso da Nijar. Badaru ya faɗi hakan ne a yayin ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai wasu muhimman cibiyoyin soja a Jihar Kaduna, ciki har da Buffalo Engineering Technical Services, Air Force Institute of Technology, da kuma Nigerian Defence Academy (NDA).

A cewar Ministan, rundunar sojin Najeriya na ƙara samun nasara a fafutukar da take yi da ‘yan ta’addan, inda ya ce an rage yawan hare-haren da ake kai wa sansanonin soja sosai. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiki tuƙuru don shawo kan barazanar tsaro da ke addabar yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta tsakiya, inda ya ce ana samun ci gaba wajen dawo da zaman lafiya, musamman ta hanyar haɗin gwiwar jami’an tsaro da gwamnatocin jihohi.

Game da rikicin da ke ci gaba a Jihar Binuwai, Badaru ya ce rikicin ya fi karkata zuwa matsalolin al’umma na kullum, musamman rikicin manoma da makiyaya. Ya ce gwamnati na aiki da al’ummomi don samar da mafita ta hanyar lumana da kuma tabbatar da cewa makiyaya suna amfani da wuraren kiwo da aka ware musu yadda ya kamata.

Badaru ya jinjina wa ci gaban da cibiyoyin soja na Najeriya suka samu a fannin bincike da ƙirƙire-ƙirƙire, inda ya ce ana yin gyara da kuma samar da sabbin kayan aikin soja a gida. Ya ambaci gyara da ƙera sabbin motoci masu kare kai daga harin kwantan ɓauna (MRAPs) a matsayin babban ci gaba. Har ila yau, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa NDA don horar da sabbin hafsoshin soja yadda ya kamata.

By ukarofi