
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya isa garin Mokwa dake Jihar Neja sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta ɗaiɗaita al’umma da sanadin rasa rayukan mutane sama da guda 200.
Haka kuma ta raba ɗaruruwan mutane da muhallansu daga ƙaramar hukumar, waɗanda a halin yanzu suke sansanonin ƴan hijira a wurare mabanbanta da suka haɗa da makarantu da sauran su.
Sauran bayani zai zo daga baya…
