
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana dalilan da suka sanya shi naɗa Ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin shugaban ma’aikata a lokacin da ya ke gwamna a Jihar Ribas.
Ya ce, ya naɗa shi a muƙamin ne a madadin ba shi kwamishinan kuɗi saboda ya sanya ido akansa.
Da fari, Wike ya yi alla-wadai da kalaman Ameachi na cewa “Dukkan mu mu na jin yunwa”, waɗanda ya yi su a lokacin bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, makon da ya gabata, inda Wiken ya ba shi amsa da cewa yunwarsa ta mulki ce ba ta abinci ba.
To saidai, Ameachi ya yi martani ga hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise a inda ya ce a matsayinsa na wanda ya bai wa Wike muƙamin shugaban ma’aikata a zamaninsa, ba ya ganin dacewar yin cacar baki da shi a idon jama’a.
Ya ce, ya (Ameachi) zama gwamna ne a Ribas bisa ƙaddarawar Ubangiji da taimakon tsohon gwamna, Peter Odili da Ma’aikatar Shari’a da kuma al’ummar jihar.
“Ku tambaye shi ta yaya ya mayar da ni gwamna. Ina faɗar wannan ne saboda ba na son yin taƙaddama da yara”, inji Ameachi.
Ya ƙara da cewa, “kun san shi ya naɗa kansa shugaban ma’aikata. Shi ya mayar da kansa gwamna. Shi ya mayar da kansa Minista. Shi ya mayar da kansa shugaban ƙaramar hukuma”, inji tsohon ministan.
