Abinda ya sa muka fifita yaƙi da miyagun ƙwayoyi – Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya ce Gwamnatin Tarayya tana fifita yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ne saboda tasirinsa mai girma akan harkar tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’umma.

Ya alaƙanta amfani da sinadarai masu cutarwa musamman akan matasa da ta’azzara da rashin tsaro ke yi a Nijeriya ganin cewa ƴan ta’adda da dama suna mu’amala da su, lamarin da ke taimaka wa yawaitar manyan laifuka da tada zaune-tsaye.

Ribaɗu ya kuma ce, gwamnati ta duƙufa wajen tallafa wa ayyukan yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da gurɓatattun magunguna domin tseratar da ƙasar daga cutarwarsu.

A lokacin da ya ke magana a wani taron jami’an hukumomin da ke da alhakin kula da lamarin, Ribaɗu ya bayyana shirin a matsayin abinda ya kere tursasawar doka kaɗai, yana mai cewa lallai akwai buƙatar al’umma su bada gudumawarsu wajen daƙile munanan ayyukan.

Ya kuma gargaɗi dilolin miyagun ƙwayoyi da cewa daga yanzu ba za sake amince wa da harkar dillancin miyagun ƙwayoyi ba a ƙasar, yana mai kira ga hukumomi da sauran masu-ruwa-da-tsaki da su taimaka wa gwamnati wajen ganin an cimma nasarar a yayin hoɓɓasan.

By Babaji