Arsenal za ta yi adabo da ƴan wasa 20 ciki har da Jorginho

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴan wasa Jorginho da Kieran Tierney za su bar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, bayan da kwantiraginsu ya ƙare a ranar 30 ga watan Yuni, 2025, waɗanda ta sanyaa jaddawalin waɗanda ba ta buƙatar su.

Jorginho, wanda ɗan wasan tawagar Italiya ne da ke dab da rattaɓa hannu a Flamengo ta Brazil, ya koma Emirates ne daga Chelsea a Janairun 2023, inda ya yi mata wasa 79.

Shi kuwa Tierney, ɗan tawagar Scotland, ya koma Arsenal daga Celtic ne kaka shida da suka gabata, inda ya buga wasa 170, kana daga baya ya je aro a Real Sociedad a kakar 2023-24.

Bayan da ya koma Emirates, ya buga wasa 13 a Premier League, sannan zai sake koma wa Celtic.

Yarjejeniyar Thomas Partey kuwa, za ta ƙare ne a ƙarshen watan Yuni, amma Arsenal na tattaunawa da shi domin tsawaita zamansa a ƙungiyar.

Har’ilayau, Raheem Sterling, wanda ya buga wasannin aro guda 28 a Arsenal, zai sake koma wa Chelsea da taka leda, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

Cikin waɗanda Arsenal ta kora har da matasan ƙungiyar ƴan ƙasa da shekaru 18 da 21 da wasu daga cikin matan dake yiwa ƙungiya wasanni.

By Babaji