Ambaliyar Mokwa: Tinubu ya amince da ware biliyan N2 da tirelolin shinkafa 20 ga waɗanda iftila’in ya shafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 2 domin sake gina baki ɗaya gidajen da ambaliyar Mokwa a Jihar Neja ta lalata.

Mataimakinsa, Kashim Shettima ne ya faɗi hakan a yayin ziyarasa a garin Mokwa a yau Laraba, biyo bayan ambaliyar da ta yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi dama tare da ɗaiɗaita ɗaruruwan mutane.

Shettima ya kuma ce, Shugaban ƙasar ya umarci a gaggauta kai tireloli 20 na shinkafa ga mutanen da iftila’in ya afka wa a ƙoƙarin gwamnatinsa na rage musu raďaďi.

Ya tabbatar musu da cewa, Shugaba Tinubu na tare da su a yayin jimamin al’amarin, sannan za a warware dukkan matsalolin da ke damun su.

Har’ilayau, ya ce Tinubu ya umarci a gaggauta gyara gadoji da magudanan ruwa da suka lalace a waurare da ambaliyar ta shafa.

Tuni dai jami’an gwamnati suke aikin bincike da ceto waɗanda suka ɓata a sanadiyyar ambaliyar, wadda ta yi dalilin tarwatsa gidaje da rasa rayukan sama da mazauna guda 200 a yayin da ta auku a ranar 28 ga Mayu, 2025.

By Babaji