Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Baban mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan harkar siyasa, Hon. Ibrahim Kabir Masari ya bayyana dalilan da ya sa suka shiga suka fita shi da Gwamna Dikko Raɗɗa aka soke aikin sake gina hanyar ƙanƙara zuwa Katsina daga hannun ɗan kwangila.
Kabir Masari ya faɗi haka ne a Katsina a lokacin bikin raba shinkafar da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar don raba wa al’umma su rage raɗaɗin rayuwa da ake fama da shi.
Aikin hanyar mai tsawon kilomita 170 da ta taso daga Marabar ƙanƙara zuwa Katsina, ta haɗa ƙananan hukumomi bakwai waɗanda yawancinsu manoma ne a cikinsu, sannan suna fuskantar matsalar tsaro daga ‘yan bindiga.
ƙananan hukumomin sune; Malumfashi, ƙanƙara, ɗanmusa, Safana, Dutsinma, Kurfi da kuma ɓatagarawa duk a jihar.
Lokaci da aka bada aikin, al’umma da dama sun nuna farin cikin matuƙa inda suka ce hakan zai taimaka wa mutane musamman manoma, sannan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen kai ɗauki a yayin da aka kai hari.
Sai dai kwatsam aka ji labarin ministan ayyuka na Nijeriya ya soke kwangilar daga hannun kamfanin da aka bai wa ita daga farko duk da cewa an fara aikin.
Hon. Masari ya bayyana wasu hanyoyi da gwamnatin tarayya ta bayat a matsayin sharuɗa inda ya ce hanyar ƙanƙara zuwa Katsina ba a ɗora ƙwarya a gurbinta ba shi ya sa suka nemi shugaban ƙasa ya soke ta.
Ana zargin cewa wani jigo a jam’iyar PDP a Katsina, kuma ɗaya daga cikin yaran Ministan Abuja, Nyesom Wike ne aka bai wa kwangilar aikin hanyar a farko wanda hakan bai masu daɗi ba inda suka shiga suka fita aka dakatar da aikin.
Da yake tsokaci game da soke kwangilar, shugaban gamayyar ƙungiyoyin Arewa, Kwamarad Jamilu Aliyu Charanchi, ya yi alla-wadai da wannan mataki sannan ya bayyana mahimmancin yin hanyar, sai dai ya ce abin baƙin ciki an dakatar da aikin saboda siyasa
Ya ce, a lokacin tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari, an sha yi musu wasa da hankali wajen ɗaukar alƙawari ba cikawa, musamman abinda ya shafi aikin hanyar Kano zuwa Katsina wanda yanzu aiki ya tsaya cak ba a san ranar cigaba ba.
Tun bayan sanarwar dakatar da wannan aiki, al’ummomi da dama ke tofa albarkacin bakinsu musamman waɗanda wannan aikin hanya ya shafa kai-tsaye. Da yawa sun yi Allah wadai da wannan mataki da Gwamna Raɗɗa da Hon. Masari suka ɗauka saboda bambancin siyasa.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko shugaban ƙasa zai sake bada aikin hanyar ga wani kamfani da Raɗɗa da Masari ke so, ko kuma shi kenan ruwa ta sha?
