Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Alhaji Abubakar Lawan Jinjiri Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙaramar Hukumar ƙiru, ya bayyana cewa ɗaruruwan magoya bayan ‘yan jam’iyyar APC ne suka dawo jam’iyyar su ta NNPP saboda gamsuwa da aƙidar kawo cigaba ta jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a lokacin da ya jagoranci waɗanda suka sauya sheƙa yin mubaya’a ga jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa dake kan titin Mila.
Ya ce shi yasan yaro da jagoransu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya tura karatu ƙasar waje alhali iyayensa basu da kuɗin da za su biya wa kansu su je ko da Abuja, amma sai ga ɗan su ya je Indiya ya yi karatu ya zama Injiniya yanzu yana aiki yana taimakon iyayensa da makota da al’ummarsu, inda ya ce akwai irin waɗannan da yawa.
Ya ƙara da cewa ganin irin raya cigaban al’umma da raya ƙasa da kyakkyawan nufi da na zuciya da Kwankwaso yake da ita ake gani a aikace a fannoni daban-daban shi yasa mutane ke ta tururuwar shigowa cikin tsarin tafiyar Kwankwasiyya.
Ya ce ga waɗanda suka shigo jam’iyyar NNPP a yanzu tsarin Kwankwasiyya duk an zama abu ɗaya da waɗanda suka samu a ciki kuma tun daga mazɓba har ƙaramar hukuma za a yi musu adalci kamar yadda jagora ya tabbatar masu.
Alhaji Abubakar Jinjiri ya ce duk jiga-jigan ‘yan hamayya a kiru suna waje daya suka zo da. NNPP suka ci sanata da ɗan majalisar jiha da na tarayya a yankin ƙiru Abba Kabir Yusuf ya ci Gwamna Kwankwaso ma ya ci zaɓen shugaban ƙasa basu taɓa faɗuwa ko akwati ɗaya ‘yan hamayya ba sa ci dama mun fi ƙarfinsu basu sun mutu mushen gizaka ne.
Shi ma jagoran Kwankwasiyya na ƙaramar hukumar Kiru, Hon. Bello Aliyu ƙiru ya ce mutum 1,673 ne suka dawo jam’iyyar NNPP daga mazaɓun 15 ƙarƙashin dattijai guda biyu da matashi guda ɗaya. Alhaji Lawan ɗalha shugaban dattawa na APC na ƙiru da tsohon ɗan majalisa a jamhuriya ta biyu Alhaji Aminu Lawan lwanar Dangora Dattijo ne mai kyakkyawan mu’amala da ya san jiya da yau.
Ya ƙara da cewa akwai kuma shugaban matasa da a baya suka bi wani mutum mai son biyan buƙatar kansa sai daga baya suka farga suka dawo ƙarƙashin Mahmud Tela Kwanar ɗangora sune jagorori da suka jawo wadannan dinbin tsofaffin yan APC suka dawo cikin gidan Kwankwasiyya me daraja.
Hon. Bello Aliyu ƙiru ya ce akwai ma tsohon sakataren ilimi na ƙiru Balarabe Zubairu mai hoto da tsohon sakataren mulki na ƙaramar hukumar ƙiru yanzu sun dawo gidan Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
