Dalilin da ya sa Sanata Hanga ya ce Buhari ya juya masa baya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wani ƙusan ɗan siyasa a Jihar Kano, Sanata Rufa’i Sani Hanga, ya bayyana cewa ya kashe sama da Naira miliyan 100 daga aljihunsa wajen ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa, amma sai aka wayi gari Buhari bai yi da shi.

Da yake jawabi a Kano, Hanga ya ce da daman waɗanda suka dafa wa Buhari ya samu ɗarewa kujerar shugabancin ƙasa, duk an wata musu ƙasa a ido. Yana mai cewa, yanzu Buhari ya zaɓi wasu ne daban suke kewaye da shi waɗanda ba su bai wa yaƙin neman zaɓensa gudunmawa ba kuma ba ‘yan jam’iyyarsa ba.

“Na rasa gidajena, ni da iyalaina mun kusa rasa rayukanmu wajen yaƙin neman zaɓen Buhari cikin dare a yankinn Arewa ko Kudu, amma bayan da aka rantsar da Buhari sai ya maishe ni tare da galibin waɗanda suka yi masa aiki saniyar ware”, in ji Hanga.