Dalilin da ya sa yankin Kudu maso Gabas ba su shiga zanga-zanga ba – Shugabannin ƙabilar Igbo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugabannin ƙabilar Igbo sun bayyana cewa ba su goyi bayan yin zanga-zanga ba, kuma yankin Kudu maso Gabas bai shiga zanga-zangar ba, saboda a duk lokacin da aka yi, sun fi kowa tafka asara.

A cikin wata tattaunawar da Premium Times ta yi da Mataimakin Shugaban ƙungiyar Kare Muradun ƙabilar Igbo Zalla, wato Ndigbo, Damian Okeke-Ogene ya ce duk lokacin da aka yi irin wannan zanga-zanga, to za ta samu cewa ƙabilar Igbo ne suka fi saura tafka asara.

Okeke-Ogene ya ce su al’ummar Kudu maso Gabas sun yi amanna da umarnin da Shugaban Ndigbo, Emmanual Iwuanyanwu ya ba su kafin ya mutu, inda ya ce kada su shiga wannan zanga-zanga.

Iwuanyanwu ya mutu a ranar 25 ga Yuli, kafin a fara zanga-zanga. Kuma sai da ya yi kira gare su kada su shiga zanga-zanga.

Ya ce bayan Iwuanyanwu ya mutu, shi da kan sa ya riƙa jaddada kira ga ɗaukacin ƙabilar yankin Igbo har ma da waɗanda ke zaune sauran garuruwa, kada su shiga zanga-zanga.

Idan ba a manta ba, a ƙarshen watan Yuli dai Sarakunan ƙabilar Igbo sun ce babu ruwan su da zanga-zanga, sakin Nnamdi Kanu ya fi masu alheri.

Shugaban Majalisar Sarakunan yankin Kudu maso Gabas, Igwe Samuel Asadu, ya bayyana cewa sarakunan yankin ƙabilar Igbo ba su goyon bayan zanga-zangar da wasu ke shirya fatawa ta tsawon kwanaki 10, daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta.

Basarake Asadu wanda kuma shi ne Sarkin Edem-Ani Ogwugwu da ke cikin ƙaramar Hukumar Nsukka ta Jihar Enugu, ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ranar Lahadi, a Abuja.

Basaraken ya ce majalisar sarakunan su ba za ta goyi duk wani yunƙuri da wasu mutanen da ba a san takamaiman ko su wane ne ba.

Daga nan sai ya yi kira da a kwantar da hankali kuma a kai zuciya nesa. Kuma ya yi kira ga masu shirya zanga-zangar su sake tunani da nazari, su nemo wata hanyar nuna fushi ko damuwar su, amma ba hanyar da ka iya haifar da tarzoma a cikin ƙasa ba.

Asadu ya ce zanga-zangar lumana ta na bisa ƙa’ida, to sai dai kuma abin da ake tsoro shi ne kada ɓatagari su shiga cikin masu zanga-zanga su hargitsa komai.

“Rusa abin da aka ɗauki tsawon lokaci ana ginawa abu ne mai sauƙi, shi yasa mu ke yin kira da a yi haƙuri, a kai zuciya nesa a zauna kan teburin sulhu a samu mafita.”

Sai dai kuma sun yi roƙo ga Shugaba Bola Tinubu da gwamnatin tarayya a saki Nnamdi Kanu domin masu tayar da ƙayar-baya a yankin Kudu maso Yamma su daina tayar da hankula a yankin.

Idan ba a manta ba, ƙungiyar CAN ta la’anci shirin zanga-zanga, sannan ta kawo shawarwarin da za a samu mafita.

ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), ta yi kira ga hasalallun ‘yan Nijeriya masu shirin yin zanga-zanga su haƙura, su janye, kuma su bijiro wata hanyar nuna wa gwamnati fushin su, amma ba ta hanyar zanga-zanga ba.

CAN ta bada shawarar cewa a ƙara bai wa gwamnati lokaci domin ta shawo kan matsalolin da ke addabar ƙasar nan da ‘yan ƙasar.

Shugaban CAN Daniel Okoh ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, inda ya ke cewa, “ya kamata masu zanga-zanga su bijiro da wata hanya wadda ba sai an kai ga zanga-zanga ba, domin kada ɓangarori su yi amfani da zanga-zanga, su maida abin da tarzoma.

“Ya kamata a yi zaman tattaunawa, masu ƙorafi su rubuta koke-koken su, a kira tarukan game-gari a garuruwa daban-daban domin a yi koken jama’a. Duk waɗannan hanyoyi yi ne da za su iya kawo maslaha da mafiya, ba tare da an karya doka da oda ba.

“CAN ta na tare da ‘yan Nijeriya a daidai wannan mawuyacin yanayi da ake ciki na raɗaɗin tsadar rayuwa da tantagaryar yunwa.

“Mun damu ƙwarai da halin ƙunci, matsi da kuma fushin da talakawa ke kwana su na tashi da shi sanadiyyar tsadar rayuwa.

“Yawan koke-koken da mutane ke yi na nuna irin ƙarfin raɗaɗin da suke fama da shi a kowace rana. An shiga lokacin da mutane ke ta gaganiyar yadda za a samu a wayi gari a ga an kai gobe.

“To kuma yayin da muke cikin wannan halin tasku, ya na da kyau matuƙa mu kiyaye da dokokin da tsarin mulkin mu ya shimfiɗa, wato bayar da ‘yancin yin zanga-zangar lumana, domin nuna damuwa ga gwamnati.”

Sai dai kuma ya ce irin zumuɗin ƙagara a fara zanga-zanga kawai, wanda hakan ke ci gaba dai haifar da fargaba da tsoron kada abin da ya faru a Kenya da Pakistan ya maimaita kan sa.

“Kuma tilas mu waiwaya baya-bayan nan mu ɗauki darasi daga abin da ya faru yayin zanga-zangar #ENDSARS da ‘RevolutionNow. Saboda da farko zanga-zanga ce mai nuna fitowa a bayyana damuwa kan halin da ake ciki, amma daga baya ɓatagari su ka mayar da ita mumnunar tarzoma,” inji shi.

By ukarofi