Dalilinmu na kama jami’an NAHCON – ICPC

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Rashawa da Ayyukan da Suka Saɓa ƙa’ida ta Nijeriya (ICPC) ta bayyna dalilan da suka saka ta kama wasu manyan jami’an Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON).

Hukumar ta ce, ta kama su ne bisa zargin su da karkatar da kuɗaɗen tallafin aikin Hajjn 2024 har Naira Biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar.

An damƙe jami’an ne a ofisoshinsu tare da kai su ofishin hukumar biyo bayan rashin amsa gayyatar da ICPC ta yi musu a baya.

Wani babban jami’i a hukumuar ya tabbatar da kamen, amma ya ce tuni aka bayar da belin su kuma suna taimaka wa hukumar da bayanai.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ta ce mutum ɗaya ne aka gayyata.

Bayanai sun nuna cewa hukumar na neman bahasi ne game da yadda aka kashe naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa Nahcon a matsayin tallafi ga mahajjatan Nijeriya a ibadar 2024 da aka kammala a watan Yuli.

Tun da farko naira miliyan 4.9 ne hukumar ta tsayar a matsayin kuɗin kujerar zuwa aikin Hajjin da maniyyata za su biya, amma sai ta mayar da shi miliyan shida da 800,000 tana mai ɗora alhakin kan karyewar darajar naira.

A wannan yanayin ne kuma rahotonni suka ɓulla cewa gwamnatin tarayya ta tallafa da biliyan 90, wanda hukumar ta ce ta rarraba su tsakanin alhazai 5,447 da suka tafi ta hannun gwamnati.

Tun a ranar 30 ga watan Yuli ICPC ta gayyaci shugaban NAHCON, Jalal Arabi, domin ya yi mata bayani game da yadda hukumar ta gudanar da aikin Hajjin na bara.

Wata sanarwa daga hukumar ta ce an gayyace shi ne kawai bisa tsari kamar yadda hukumar ta saba yi duk bayan kowane aikin Hajji.

“Duk da cewa gayyatar tasa za ta haifar da fargaba a zukatan abokan hulɗa, hukumar na tabbatar da abu ne da aka saba yi domin kare kadarorin al’umma kuma bincike ba shi nufin aikata laifi,” a cewar kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara.

Mataimakin darakta a sashen hulɗa da jama’a na ICPC, Hassan Salihu, ya bayyana cewa daga baya sun gayyaci ƙarin jami’ai, waɗanda ta kama a yanzu bayan “sun ƙi amsa gayyatar”.

Sai dai bai bayyana sunayensu ba.

“Da a ce sun zo lokacin da aka gayyace su za mu cigaba da yin binciken cikin sirri kamar yadda aka saba yi a duniya,” inji shi, “to taurin kai da raina hukuma ne ya sa aka kamo su, amma an bayar da belin su.”

Da aka tambaye shi game da sunayen mutanen da suka nuna turjiyar, ya ce, “Tsarin doka bai bayar da dama a bayyana sunayensu ba.”

Sai dai mai magana da yawun NAHCON, Fatima Usara, ta ce mutum ɗaya ne hukumar ta “gayyata”.

“Mutum ɗaya ne kuma shi ma bai kai matsayin darakta ba,” a cewarta.

“An gayyaci daraktocinmu duka kuma sun amsa gayyatar. Mutum ɗaya na sani wanda bai amsa gayyatar ba kuma suka zo suka tafi da shi.”

By ukarofi