Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dambarwar dakatacciyar ‘yar Majalisar Dattawa mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ɗauki sabon salo, inda ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da haɗa baki da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, domin kashe ta.
Natasha ta kuma bayyana cewa dukkan mutanen biyu ne ke da hannu wajen sake dawo da ƙarar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shigar.
Akpoti-Uduaghan ta yi wannan zargin ne a lokacin da take jawabi ga ɗimbin magoya bayanta a taronta na dawowa gida a Kogi ranar Talata.
Ta ce, “Bari na faɗi haka a yanzu, a ranar 14 ga Maris… Ku tuna, kwanan baya, wato ranar 12 ga watan, Akpabio ya gana da Gwamna Ododo, inda ya buƙaci a kirani, amma ya ce masa ba zai yiwu ba, domin talakawa suna tare da ita, jama’a na tare da ita.
Ta ce, martanin da Ododo ya bayar bai yi wa Akpabio daɗi ba don haka ya aika a kirawo magabacinsa Bello wanda wani Sanata ya tuƙa shi daga otel ɗin Hilton domin ya gana da shi.
“An sanar da ni komai, ganawar sun kasu kashi biyu ne, suka ce masa ya fara kirana kuma zai ba da kuɗi. Tabbas abubuwa sun kisa canjawa a wannan daren, abu na biyu da ya ce masa shi ne ya yi ƙoƙarin kashe ni, amma ya tabbatar kisan bai faru a Abuja ba, sai a Kogi, wanda zai yi kamar mutanen gari ne suka kashe ni” inji Akpoti-Uduaghan
Ta bayyana cewa ba ta faɗa lamarin komai ya sani a lokacin ba, amma ta tabbatar da cewa an sanar da hukumomin tsaro.
Ta kuma bayyana yadda Akpabio ya cire ta daga kwamitin majalisar dattawa.
Ta ce, “A cikin kalamansa, ya ce, ‘Ta yaya za a kai irin waɗannan albarkatun na Neja-Delta zuwa Arewa, har ba ku hana ba?’ Saboda ayyukan man fetur guda biyar ne Akpabio ya cire ni daga kwamitin kula da harkokin mai.
Shi kuwa wani ƙwararren likita, Dr Aleɗ Adekunle, ya bada shawarar a duba lafiyar ƙwaƙwalwar Sanata Natasha bisa zargin da ta yi wa shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Kwararren likitan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, 2025 ya zargi Sanata Natasha da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa kan tuhume-tuhume mara tushe bare makama a kan fitattun mutane a cewarsa.
Dokta Adekunle a nasa ra’ayin, ya bayyana cewa akwai buƙatar a yi la’akari da yiwuwar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa a ɓangaren Sanatar da aka dakatar.
Dr Adekunle ya kuma buƙaci Sanatan Kogi da aka dakatar da ta nemi kulawar da ta dace cikin gaggawa.
“Lokacin da na fara kallon faifan bidiyon Natasha Akpoti tana zargin Sanata Godswill Akpabio da tsohon Gwamna Yahaya Bello da yunƙurin kashe ta, tun da farko na yi matuƙar kaɗuwa kamar kowane ɗan Nijeriya, shi ya sa nake shawarta Natasha ta je a duba ƙwaƙwalwarta cikin gaggawa.”
A gefe guda kuma, Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba.
INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadar ba.
Wannan sanarwa ta fito ne daga shafukan sada zumunta na INEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025.
Wasu ƙungiyoyi sun yi ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha kiranye, wanda suka ce Sanatan na neman jefa su cikin rikicin da ka iya hana su samun romon dimokuraɗiyya.
ƙungiyoyin sun miƙa ƙorafinsu ga INEC bisa hujjar cewa ba ta yi musu wakilci mai kyau ba.
Sun yi iƙirarin tattara sama da sa hannun mutum 250,000 daga cikin masu kaƙa ƙuri’a kimanin 480,000 da ke yankin.
Sanata Natasha, ta fuskanci ƙalubale a siyasa a baya-bayan nan, ciki har da dakatarwar tsawon watanni shida d Majalisar Dattawa ta yi mata bisa zargin aikata rashin ɗa’a.
Ta ƙalubalanci wannan hukunci, inda ta bayyana cewa an dakatar da ita ne saboda zargin cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Wannan batu ya haddasa muhawara mai zafi kan haƙƙin mata da yanayin siyasar Nijeriya.
Yadda INEC ta yi watsi da buƙatar tsige ta na nuni da tsauraran sharuɗan da ake buƙata kafin batun kiranye ya samu ƙarbuwa.
Wannan yana jaddada yadda ake buƙatar bin dokoki da tsari kafin a iya aiwatar da yi wa wani ɗan majalisa kiranye.
Sai dai a martaninta kan gangamin da Natasha ta shirya duk da dakatarwar hukumar ‘yan sandan jihar, gwamnatin Jihar Kogi a ranar Talata ta ce taron gangamin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan maraba da ganawa da ta yi da su ya saɓa wa dokar hana taron siyasa da gwamnatin jihar ta saka.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a ranar Talata cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Kingsley Fanwo, ya yi don mayar da martani ga Mrs Akpoti-Uduaghan da magoya bayanta.
A yayin da Natasha ke shirin dawowa jihar Kogi, gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sandan jihar sun fitar da sanarwa kan haramta taron saboda dalilai na tsaro.
‘Yan sanda sun sanar da masu shirya taron gangamin kan su janye shirinsu saboda rahotanni da suka samu na ɓata-gari na shirin haifar da yamutsi a wurin.
Sai dai sanatar wacce aka dakatar a majalisar dattawa tare da magoya bayanta sun ƙi yin biyayya ga wannan umarni.
Natasha ta ce ba ta saɓa wata doka ba tana mai cewa, “muna da ‘yancin zuwa duk inda muke so mu kuma gudanar da taruka da shagulgulan biki.”
Duk da haka, Mista Fanwo na ganin sanatar ta karyar dokar hana gudanar da tarukan a jihar.
“Wannan sanatar da aka dakatar da ita, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sha yin abubuwa da suka ci karo da doka. Wannan taro da ta yi duk da umarnin ‘yan sanda, ya nuna kasancewarta barazana ga harkar tsaro a jihar.
“Tana sane ta karya dokar gwamnatin jihar na haka tarukan siyasa wanda aka sa domin samar da zaman lafiya. A yayin da aka bayyana mata laifin da ta aikata, kamar kullum, sai ta ɓige da amfani da dabaru da zarge-zarge marasa tuhsne.
A yayin da take gab da isa jihar Kogi, Natasha ta yi wani rubutu a shafinta na Facebook tana mai zargin gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, da shugaban majalisar waɗanda ta ce duk abin da ya same ta su ne.
A cikin rubutun wanda daga baya ta goge, Natasha ta rubuta cewa, “ya ku mutanen jihar Kogi, ina fatan za mu yi bikin sallah lafiya a yau. Sai dai idan wani abu ya same mu, muna alƙanta hakan da gwamna Ododo da Yahaya Bello da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Gwamnan jihar mai ci, Ododo da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, sun fito ne daga yanki ɗaya da Mrs Akpoti-Uduaghan.
Natasha ta zama sanata a watan Nuwambar 2023 ne bayan samun nasarar a kotu. Ta maye gurbin Sanata Abubakar Ohere, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓe a ranar 25 ga watan Fabarairu.
A ranar 6 ga watan Maris ne aka dakatar da Sanata Natasha ‘yar jam’iyyar PDP na tsawon watanni 6 daga majalisar dattawa bayan shawarar da kwamitin ɗa’a da karɓar ƙorafe-ƙorafe a majalisar ya bayar.
Wannan mataki na zuwa ne biyo bayan ƙin yin biyayya ga tsarin sauya wurin zama da aka yi mata a ranar 20 ga watan Fabarairu.
Sauran matakan da majalisar ta ɗauka a kan Natasha sun haɗa da haramta mata zuwa majalisar da ayyana kanta a matsayin ‘yar majalisa da kuma janye mata jami’an tsaronta da rufe ofishinta.
Hakazalika, majalisar ba za ta biya ta albashinta ko alawus-alawus ɗinta ba na watanni shida. Sai dai majalisar ta nuna yuwuwar janye dakatarwar idan Natasha ta ba da haƙuri.
A makon da ya gabata ne aka yi yunƙurin yi wa sanata Natasha kiranye a ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Concerned Kogi Youth and Women, wacce ta shigar da kokenta ga hukumar zaɓe, INEC.
A cikin wasiƙar da ƙungiyar ta aike wa da Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ta nuna rashin ƙarfin guiwarsu kan wakiliyar tasu tare da neman INEC ta fara shirin yi mata kiranye.
Sai dai hukumar INEC ta gano kurakurai da aka tafka a takardun da aka kawo mata ɗauke da sa hannun mutanen mazaɓar Natasha da ke son a yi mata kiranye. Takardun dai babu bayanan adireshi da lambar waya da imel na masu koken.
Kwana ɗaya bayan nan, hukumar INEC ta sanar da cewa ta samu bayanan waɗanda suka shigar da koken daga ƙungiyar kuma a shirye take ta fara ɗaukar matakin kiranyen.
Sai dai har yanzu majalisar dattawa ba ta ce komai ba game da samun sanarwar fara kiranyen Natasha ko akasin haka.
A wani martani da Mrs Akpoti-Uduaghan ta yi, ta yi Alla-wadai da shirin kiranye da ake yi mata wanda ta ce na ƙarya ne.
Sannan ta jaddada matsayinta kan dakatar da ita da aka yi na watanni shida cewa an yi hakan ba bisa ƙa’ida ba kuma an siyasantar da lamarin.
“Duk da barazana da dakatar da ni ba bisa ƙa’ida ba da yunƙurin yi min kiranye na ƙarya, ina nan a kan bakana na yunƙurin lalata da shugaban majalisar dattawa, sanata Godswill Akpabio ya yi,” Natasha ta rubuta.
A baya dai, Manhaja ta rawaito muku yadda ‘yan mazaɓar Kogi ta tsakiya suka yi Alla-wadai da dakatar da sanata Natasha daga majalisar.
‘Yan mazaɓar Natasha sun nuna damuwarsu game da rashin samun wakilci a majalisar har na tsawon watanni 6.
