Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya yi barazanar ƙwace lasisin rijiyoyin mai daga hannun masu shi da suka kasa bunƙasa shi.
Hakan dai ya saɓa wa tsarin gwamnatin tarayya na yin kira ga kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa da ke aiki a Nijeriya da su ƙara ƙaimi a fannin mai da iskar gas na ƙasar, tare da jaddada cewa gwamnati mai ci ta samar da duk wani abin da ya dace don tabbatar da gudanar da ayyuka cikin aminci.
Yayin da Gwamnatin Tarayya ta tsara shirin haƙo ganga miliyan 2.06 a kowace rana a shekarar 2025, Lokpobiri ya ce gwamnati za ta fara aiwatar da tanade-tanaden “haƙo mai ba dare da rana” na dokar masana’antar man fetur a daidai lokacin da ake ƙoƙarin bunƙasa haƙo mai.
Ya zuwa watan Fabrairun 2025, Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya ta bayar da rahoton haƙo mai a ganga miliyan 1.67 a kowace rana.
Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Mista Nneamaka Okafor, ta fitar a ranar Talata, ta ce Sanata Lokpobiri ya bayar da gargaɗin soke lasisin a wani taron aungiyar masana’antar mai da aka gudanar a birnin Florence na aasar Italiya, wanda IOC da ke aiki a Nijeriya suka shirya.
