Ina alfahari da alaƙata da Tinubu – Buhari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya ce yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu, Bola Ahmad Tinubu.

Buhari ya bayyana haka ne a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce Buhari da Tinubu sun gana ta wayar tarho a ranar Juma’a, inda a ciki Buhari ya yi Tinubu addu’ar tsawon rai da ingantacciyar lafiya da, sannan ya yi masa fatan samun nasarar a mulkinsa.

“Idan muka yi wa shugabanninmu addu’a, muna yi wa kanmu ne. ƙasarmu na buƙatar addu’o’inmu,” inji Buhari a ganawarsa da Tinubu.

Tsohon shugaban ya ce shi da iyalansa suna godiya ga Tinubu da sauran jagororin jam’iyyar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen kafa jam’iyyar APC, inda har ya samu nasarar zama shugaban ƙasa har sau biyu, bayan bayan ya sha gwadawa a baya ba tare da samun nasara ba.

“Lokacin da ‘yan Nijeriya suka zaɓi APC a 2025, zaɓi suka yi domin tsara dandamalin gina sabuwar Nijeriya inda talakawa za su samu damarmakin da suke buƙata, kuma ina jin daɗi har yanzu ba a kauce daga tsarin ba.”

By ukarofi