Dandalin Shawara: Ina son in hana matata aiki don ba na cin komai daga abinda take samu

Spread the love

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malama Aisah da farko ina neman ahuwa kan aiko da sako ta murya ba ta rubutu ba. Ni dai matsalata guda zuwa biyu. Matata tana aiki don malamar makaranta ce. To matsalar dai ita ce, ko dannan zuwa can ba ta so ta yi mani nasiha akan sha’anin gida. Bansan ranar da ta siye ko sabulu a gidan ba da niyyar rage min ɗawainiya. Kuma ko Naira biyar na ara to hankali bayya kwanciya sai na biya ta ita. ko yaranta ma ba abinda take iya yi masu cikin albashinta.

Kwanaki ma wasu kuɗi gwamnati ta ba su ko rance ne ko kyauta ban sani ba, amma a ranar ma magin da za a sa a miya sai da aka yi jira na na dawo daga gareji inda nake aikin gyaran mashi sannan na bayar kafin a dafa miyar. 

Shawarar da nake nema ita ce guda biyu. Ta farko zan so ki ja kunnen mata da ke irin wannan hali na matse wa mazajensu nasu aljihu da rashin taimakonsu. Na biyu kuma ina neman shawarar yadda zan yi, don gaskiya ba zan iya barin ta ta ci gaba da yin aikin ba alhali ba na amfana da komai ciki, don ai ni karan kaina na mata ƙoƙari da nake haƙura da wasu buƙatu don na san ta tafi aiki, amma kuma a ce duk abinda ta samo daga ita sai ita.

Abu na farko na san idan na hana ta aikin za mu samu babbar matsala, kuma danginta za su yi ca kaina don su suka tsaya dole sai ta yi aikin. 

Ki ba ni shawarar mafita don Allah. Na gode ƙwarai, Allah Ya saka da alheri. Ni ne…………..daga nan………..na gode, na gode. Ma’asalam.

AMSA: Wa’alaika salam. Kafin na kai ga ba ka shawara kamar yadda ka buƙata, zan so na ɗan tunantar da kai wani abu da nake hasashen ka san da shi, wato haƙƙin kula da iyali. Kamar yadda ka sani, lokacin da aka ba ka matarka aure, wasu nauyi sun hau kanka, wato ci da sha da sutura da kuma mu’amalar aure.

Yayin da ake wannan bayanin ba ruwan mai faɗa ko ince addini da neman bayanin matarka na daga dukiya, ba za a tambaye ko ita mai digiri ba ce, ko ita ‘yar kasuwa ba ce da sauransu. Dalili ba shi da alaƙa da nauyin da ya rataya kanka. Wato dai ‘nata nata ne, naka naku ne’.

Bari mu koma kan neman shawarar da ka yi, da farko zan so ka dinga tuna cewa, babu dole matarka ta yi maka wata hidima ta gida, kyautatawa ce kamar barinta ta yi aiki ma kyautatawa ce daga wurin ka.

Akwai wasu matsaloli da ke biyo baya a lokuta da dama ko ince a aure da dama wanda mace ke ɗaukar ɗawainiyar wani ɓangare a buƙatun gida, musamman a ƙasar Hausa.

Abin nufi anan shi ne, idan har mace ta samu damar ɗaukar ɗawainiyar wasu buƙatun gida, ba duka mata ba amma kaso mai yawa za su ji sun kawo fa, don haka akwai wasu ababe da ya kamata a riƙa ɗaga masu kafa, kamar misali, mace na kaso 50 bisa 100 na lalurar gida, tambaya irin waɗanda mazan Hausa ke wa matansu idan sun jima ba su dawo gida ba ko hanasu fita da makamantansu za su zama ababen da za ku iya samun matsala kansu.

Iko da isar da kake iya nuna mata a matsayin mijinta da yawa za ka rasa su, sai kuwa inkayi dace da maccen da ke kusa da aljanna.

Ba wai ina kokarin nuna cewa matarka ta kyauta ba, ko kaɗan bata kyauta ba, domin kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa a littafi mai tsarki, “Sakamakon kyautatawa na ga kyautatawa”. Idan ka bar ta ta yi aiki, wanda ba dole ne ka bar ta ba matuƙar ba wani alƙawarin yin hakan da ka ɗauka kafin a baka aurenta, to fa ya kamata a ce ita ma ta dubi kyautatawar ta saka ma da yin wasu ababen da za su ɗan sauƙaƙa buƙatun.

Yadda rayuwa ta yi wahala a wannan zamani shi ya sa ake ta kira ga mata su tashi su nemi na kansu don a samu sauƙi a buƙatun gida, ba wai don su tara su yi ta ɓoyewa sai ranar biki ba.

Babban kuskure da mata ke yi a wannan lokacin bai wuce ki samu ki ƙi taimakon gidanki, a cewar zugar da shaiɗan ke yi maki, idan ki ka gwada yin wasu buƙatu zai bar ki da su, hakan na nufin ya fara tunanin damar ƙara aure. Shin a tunaninki duka mazan ne suka zama shashashu ko kuwa shi za ki yi wa ba Allah ba?

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

By ukarofi