Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi na Kwalliya. Sannunku da jimirin bibiyar mu.
A wannan karon shafin zai yi duba ne kan sha’anin fata wadda ta kasance uwa ga kwalliya, kyanta kan yi tasiri kan kowacce kwalliya, idan kuwa ba ta samu kulawar da ta dace ba ba ta yadda kwalliya zata yi armashi.
Kula da fata ba kawai wanke ta da shafa mata mai ne kawai ba, za mu iya cewa wata cikakkiyar al’ada ce da ya kamata a mayar jiki, wadda ta haɗa da tsafatacce fata cikin hikima, tsaftar muhalli, da zaɓaɓɓun salon rayuwa da fatar ke maraba da su.
Idan aka bi hanyoyin da suka dace tare da kiyaye ƙa’idoji yadda ya kamata, tabbas fata zata kasance cikin ƙoshin lafiya, hakan na nufin samuwar sheƙin ta tare da jure matsaloli irinsu ƙuraje, bushewar fata da tsufa da wuri.
Kada na cika ku da surutu, bari mu je zuwa ga darasin namu, hanyoyi 10 na kula da fata. Saidai kafin nan, zan so in jawo hankalinmu kan cewa waɗannan hanyoyi fa ba su kaɗai ba ne, saidai mun zaɓo mafi muhinmanci daga cikinsu. Ga su kamar haka:
1. Tsaftace fata:
Kamar yadda muka sani tsafta ita ce ginshiƙin kowacce kyakyawar fata, kuma idan babu ta ba yadda kwalliya za ta yi tasiri.
Ya kasance ana wanka a ƙalla sau biyu a rana, idan kuwa hakan zai yi wuya, ita fuska kada a bari ta kasa samun wannan kulawa, ta hanyar amfani da sabulun wanke fuska da ya dace da fatar. Koda wankan zai samu safe da yamma, a kula da irin abinda ake amfani da shi ga fuska. Domin ita ce ta fi ɗaukar kwaramniyar kwalliya da irin kayan da ake shafa mata, rashin wanke ta yadda ya kamata zai iya haifar da matsaloli da dama.
2. Shafa man fata akai-akwai (Moisturizer):
Amfani da man da ya dace ga fata na kawo kariya ga fatar, sannan yana taimakonta wurin bayar da irin sakamakon da mai ita zai yi farin ciki da shi. Hakan kuwa zai iya samuwa ne kaɗai idan kin yi amfani da irin man da fatarki ke buƙata (idan kina da busashiyar fata man da za ki yi amfani da shi daban da mai fata mai matsƙi. Haka kuwa akwai fata mai rauni wadda abu kaɗan ke iya mata illa don haka mayuka masu ƙarfi duk yadda suke da kyau kan iya yi mata lahani. Ita kuma mai ƙarfi daga fata za ta iya ƙin bayar da sakamako a lokacin da aka yi mata amfani da mayuka marar ƙarfi).
