Dandalin Shawara: Ina yawan saka turare, amma mijina na yawan cewa ina wari

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Asas don Allah ki sanar da ni yaya zan yi, Allah Ina yawan amfani da turare sosai, saidai duk yadda na yi wanka na saka turare, idan mijina ya kusance ni sai ya janye wai ina wari ba zai iya kusanta ta ba. Idan na ce ga hi ina ƙamshin turare, sai ya ce, ba wannan yake nufi ba. Kuma har ga Allah ban fahimce shi ba, kuma ya ƙi yin bayanin da zan gamsu. Har na fara tunanin ko magani ne aka yi na raba mu. Yanzu mun kusa wata biyar daƙyar yake kusanta ta. Ki taimaka min da yadda zan shawo kan lamarin.

AMSA: Waalaiki salam. A iya fahimtar da na yi wa tambayar ki, zan iya cewa mijinki na ƙoƙarin sanar da ke gaban ki na wari ba wai jikinki ba, wanda komai yawan turaren da za ki saka ba zai hana makusancin ki jiyo warin wurin ba.

A ‘yan satukan da suka gabata, munyi darasi na musamman kan warin gaban mace a shafinmu ma Kwalliya, wanda zan ɗan tsakuro bayyanan kaɗan daga can;

Gaban mace wuri ne da ke ɗauke da wani nau’i na ƙamshi da ya saɓa wa wanda gangar jiki ke fitarwa. Wannan ƙamshi dai a wurin wasu suna kiran sa da wari wanda ba a son jin sa, wannan dalilin ne ke sa wasu har turare suke sanyawa a gabansu don kawar da wannan ƙamshin marar daɗi a wurin su (hakan kuwa kuskurene, kuma yana janyo ciwo). Kaɗan ne suka fahimci cewa, wannan launin iska da ke fita bai zama abin ƙyama ba matuƙar dai an yarda da na jiki ma bai da illa. Kamar yadda aka sani, kowane ɗan adam na da yanayin ƙamahin jikinshi, wanda kare ma da shine yake bambanta mutane.

Sai dai wasu dalilai kan sa wannan ƙamsahin na gaba gauraya da wasu abubuwa da muke janyowa, to a lokacin ne zai yi sanannen wari da kowa ke ƙyama.

Warin gaban mace na ɗaya daga cikin manyan ababen da ke kawo wa mata matsala a gidan aure, domin illolin sa masu yawa ne, tun daga yadda zata dasa ƙyamar ta a wurin mijinta, kasancewar ba wanda yake son jin wari a tare abokin mu’amala irin wannan, ga uwa uba ni’imar mace da yake iya yin nasarar kawarwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Warin gaba yana samuwa ta dalilai da dama, kamar rashin tsafta, wadda ta haɗa da riƙon sakainar kashi da abokan tu’ammalin sa, kamar wando. Rashin damuwa da tsaftar kamfai da muke amfani da shi, ko rashin yin amfani da shi a lokuta fita ko tafiya a ƙasa wadda zai sa duk wata ƙwayar cuta da ta samu damar ratsa tsakanin ƙafafuwanki zata kai gare shi, hakan zai sa su taru su haddasa ma ki warin gaba.

A wani lokacin wasu kayan mata na zama silar samuwar warin gaba, saboda ababen da aka haɗa su ba masu tsafta ba ne, ko kuma ma kayan haɗin karan kansu ba su dace ayi amfani da su a wurin ba.

Yayin da maigida ya kusance ki, bayan kun kammala, wasu matan na da ɗabi’ar gyara kwanciya, su yi barci, har sai sun tashi salla ne za su wanke wurin. Wannan maniyi da ya fito zai samu awanni a wurin, shi ma zai iya zama silar warin gaba, idan aka mayar da shi ɗabi’a.

Rashin damuwa da inda za mu yi tsugunni na daga banɗaki, shi ma zai iya zama hanyar samuwar warin gaba. A taƙaice dai warin gaba samun sa ake yi ta sanadiyyar wasu nau’in ƙwayoyin cuta da ya kamata mu kawar cikin lokaci ko mu hanasu zuwa wurin, jinkirin zai haifar da wannan matsala ta wurin gaba. Kenan za mu iya saka cutar ɓaginitis wadda muka fi kira da ciwon sanyi a layin. Domin yana ɗaya daga cikin alamomin da ke nuna ciwon sanyi ya samu gurbin zama, wato warin gaba.

Kuma ya kamata mata su san cewa, warin gaba ba halitta ba ce, domin wasu matan kan kafa hujja da cewa, haka aka haife su da shi kamar warin ƙashi, wannan ba gaskiya ba ne, sai dai jimawar sa a jikin mace zai sa ya yi ƙarfin da zai yi wuyar jin magani.

Anan zan iya cewa, shawara ta farko ita ce, ki ajiye hankalinki ki tabbatar ko hasashen da muka yi gaskiya ne, ta hanyar tabbatar da kina warin ne. Idan kin tabbatar, za ki ajiye hankali ki yi nazarin ɗabi’ar da ki ke yi da ta haddasa maki warin.

Idan ciwon sanyi ne, sai a fara da maganin da zai kawar da shi, wanda kina da zaɓi a na turawa da Hausa.

Idan kuwa wasu daga ciki ko ƙari daga abinda muka ambata, to za a fara da barin ɗabi’ar ne, kafin a bi hanyoyi waɗanda da yawa daga ciki masu sauƙi ne, kamar amfani da kanumfari, ko haɗin magarya, ko na sassaƙen ɓaure da miski don ganin an kawar da warin. Kuma akan samu ingantattun magani da za a iya amfani da su, daga na Turawa har na Hausa da zai iya samar da abinda ake buƙata.

By ukarofi