Yaƙin Gaza ya zama na ƙare dangi

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun ana faɗa tamkar kambama magana na kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa daga Isra’ila kuma ya zama daga ɓangaren Falasɗinawa, haƙiƙa abubuwan da ke faruwa yanzu a Gaza daga hare-haren Isra’ila sun tabbatar da wannan hasashe ko ikirarin. Sai na so shiga wani darasin don fayyace bayanai sai wani abu ya sake ɓullowa daga Isra’ila ko Gaza. Shin akwai yadda za a iya raba al’ummar Gaza da Hamas? Shin ‘yan Hamas aljanu ne ko Falasɗinawa ne? Ina ganin Isra’ila ko gwamnatin Netanyahu ba za ta daina kai hari kan Gaza ba sai lokacin da ta samu damar mamaye yankin ya koma ƙarƙashin ikon ta da kuma tsugunarda Yahudawa a yankin kamar yanda ta yi wa wasu yankunan na Falasɗinawa.  Dama a tarihi kamar yadda na saba ambatawa an kirkiri ƙasar Isra’ila daga yankin Falasɗinawa ne kuma a ka kyale Yahudawa na neman maida Falasɗinawa tamkar bayin su.

Da alamu Falasɗinawa sun zama ‘yan bora ba su da gata a tsakanin ƙasashen duniya. Duk manyan ƙasashe da za su iya kai mu su ɗauki na mara baya ga Isra’ila ko abun da za su iya kawai shi ne kira na a tsagaita wuta a bar kayan agaji na shiga yankin Gaza. Hatta ma daga ƙasashe biyu da ke jagorantar sulhu wato Masar da Katar ba wani sabon bayani na matsa lamba a dawo teburin tattaunawa. Ba mamaki su ma kamar sun yi iya ƙoƙarin su ne ko an yi mu su magana ta bayan fage cewa su kau da kai. Shiga lamarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na buƙatar Falasɗinawa su ƙaura daga Gaza da sunan za a samu damar sake gina yankin. Wannan matsaya a gaskiya ƙasashen Larabawa sun yi Allah wadai da ita amma a hankali abun da Isra’ila ke neman tabbatarwa kenan. Tun da har ma babban shugaba a duniya ya kawo wannan matsaya ai Benjamin Netanyahu zai fake da ita wajen cigaba da hare-hare kan yankin da yawancin sa ma a rugurguje ya ke.

Don wahalar da su ke an samu wasu mazauna Gaza da su ka gudanar da wata zanga-zanga ta kin jinin Hamas da tsammanin in sun kori mayaƙan shikenan Isra’ila za ta tsagaita ƙarƙashe su. Wato masu zanga-zangar na ɗaukar Hamas ke jawo mu su fitina. Akwai kuskure a wanann tunanin don abun da ke faruwa a zahiri shi ne kawar da Falasdinawa daga ƙasar su don kafa karin matsugunan Yahudawa. In an duba ma akasarin waɗanda boma-boman Isra’ila su ka kashe mata ne da kananan yara da ma tsoffi. Kuma idan Isra’ila ta zo kawo hari ba ta tantance da’irar harin don majinyata a asibiti harin na shafar su. Idan da ‘yan Hamas Isra’ila ke yaƙi ya dace ta tantance harin da za ta sauke bom da wanda za ta tura sojoji ta kasa su shiga ko da asibitocin ne don kwaƙulo mayaƙan. Don raina jinin Falasɗinawa Isra’ila kan yi kan mai uwa da wabi yayin kai hari. Ko nuna tausayi ma ba ta yi in an kawo bayanan ‘yan jarirai ma sun mutu a sanadin hakan. A gani na ran dan Isra’ila ɗaya tak na daidai da ran dubban Falasɗinawa. A yau fa Isra’ila kan kai hari cikin Lebanon har ma babban birnin ƙasar Beirut ba tare da shakkar komai ba. Isra’ila ta cigaba da kai hare-hare cikin Sham duk da sauya gwamnati da kashe tasirin Iran da Hezbollah a ƙasar. Isra’ila kan kai hari cikin ƙasar Yaman. Ba wata kasa a duniya da a ka ɗore ma ta baya ta na kai hare-hare duk inda ta ke so da sunan yaƙi da makiya.

Kimanin yara 322 ne sojojin Isra’ila su ka yi wa kisan gilla a kwana 10 da su ka wuce a sabbin hare-hare da su ke kai wa tun rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas.

Hukumar yara ta Majalisar ɗinkin Duniya UNICEF ta fidda alƙaluman da karin bayanin cewa cikin yaran har da wadanda bom ɗin da Isra’ila ta jefawa asibitin Annasser na arewacin Gaza ya shafa.

Yayin da a ke kula da yara a sashen fida na asibitin sai jirgin yaƙin Isra’ila ya jefo bom da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar yara inda sauran kuma sun mutu ne a hare-hare kan tantunan da su ke maƙale a cikin su don ba su da muhalli.

Shugabar UNIECF Catherine Russell ta ce tsagaita wuta da a ka samu ya samar da fatar samun kulawa ga yaran da ke cikin matuƙar buƙatar taimako.

UNICEF ta ce tun fara yaƙin wata 18 da su ka wuce an kashe yara Falasɗinawa kimanin 15,000 inda a ka runata 34,000 kazalika a ka raba kusan yara miliyan ɗaya daga gidajen su.

Hukumar yaran ta buƙaci lallai Isra’ila ta janye dokar hana shigar da kayan agaji yankin Gaza da ta fara aiki tun 2 ga watan jiya.

Isra’ila ta kai mummunan hari kan kudancin babban birnin Lebanon, Beirut inda hakan ya yi sanadiyyar mutwar kimanin mutum 3 yayin da 7 su ka samu raunuka.

Harin na Isra’ila ya shafi wani bene ne a a yankin Dahiyeh da ke kudancin Beirut da ya zama babban mazaunin mayaƙan Hebollah.

Duk da harin na nuna keta ‘yancin ƙasar Lebanon da yarjejeniyar tsagaita wuta da Hezbollah, Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wani ɗan Hezbollah da ke taimaka ‘yan Hamas.

An ba da rahotannin harin ya shafi hawa 3 na saman benen da hakan ya nuna alamun an auna harin ne kan waɗanda a ke son hallakawa.

Har yanzu dai Isra’ila ba ta gamajanye sojojin ta daga kudancin Lebanon ba inda gwamnatin Lebanon ta tura sojojin ta da su ka maye ‘yan Hezbollah.

Isra’ila ta ƙara taƙarƙarewa kan dirar mikiya ga yankin Gaza da sunan matsa lamba ga ‘yan Hamas su sako sauran Isra’ilawa da ke hannun su tun 7 ga Oktobar 2023.

Yayin yarjejeniyarda ta wargaje ta tsagaita wuta, Hamas ta sako gomman Isra’ilawa da ke hannun ta.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce sun shiga ragargazar yankin Gaza da kai hare-hare kan mutanen da ya ke zayyanawa da ‘yan ta’adda da wargaza kayan aikin su.

Netanyahu ya ƙara da cewa ƙasar sa ta kwace yankin MORAG da ke tsakanin Khan Younis da Rafah a kudancin Gaza inda a baya wajen ya ke matsugunai da Yahudawa su ka kafa a yankin Falasɗinawa inda a 2005 Isra’ila ta janye daga yankin.

Ministan tsaron Isra’ila Israel Katz maitsaurin ra’ayi ya ce sun a son kebe wasu sassan Gaza su gwama su ga yankunan da su ka ware don tsaro.
Wannan ma sabon matakin na zuwa daidai harin da ya kashe Falasɗinawa 34 ciki har da kan ginin Majalisar ɗinkin Duniya.

Rundunar kare farar hula a Gaza ta ce hari kan ginin na Majalisar ɗinkin Duniya a Jabalia ya yi sanadiyyar kisan gilla ga mutum 19 ciki da yara 9.

Gwamnatin Falasɗinawa a birnin Ramallah ta yi Allah wadai da harin da zayyana shi da kisan kare dangi kuma hark an asibitin da Majalisar ɗinkin Duniya ke kula da shi.

Ramallah ta buƙaci lallai a matsawa Isra’ila lamba ta dakatar da wannan muguwar dabi’a ta kisa da ta ke yi.

Sabbin alƙaluma daga dawowa hare-haren Isra’ila a a ranar 18 ga watan jiya sun nuna an kashe Falasɗinawa 1,066.

In mun leƙa Sham Shugaban Sham ɗin Ahmad Al-Sharaa ya kafa gwamnati wato majalisar zartarwa ta kasar mai ministoci 23.

Wannan dai tamkar amsa kiran ƙasashen ƙetare ne da ke buƙatar kafa gwamnati da za ta ƙunshi dukkan dangogin al’ummar ƙasar.

Kazalika wannan zai kawo daidaituwar lamura da sauyi bayan kifar da gwamnatin su Al’Asad da ta share gomman shekaru ta na mulkin ƙasar ta Larabawa mai dogon tarihi.

Hakanan kafa majalisar zai kara saita ƙasar da wata kurar fitina a gabar tekun yammancin ƙasar ta yi awun gaba da ran daruruwan mutane mabiya ɗarikar Shi’a ta ALAWI da tsohon shugaban kasar BasharAl’Asad ke bi.

Gwamnatin ta mayaƙa ‘yan Sunnah ta naɗa ɗan Shi’ar Alawi Yarub Badr a matsayin ministan sufurin ƙasar.

Hakanan gwamnatin ta Al-Sharaa ta nada mace Kirista Hind Kabawat wacce ta yi hamaiya da Al’Asad kan tabbatar da mutunta mabiya addinai; a matsayin ministar jin daɗin jama’a da kwadago.

Al-Sharaa ya aiyana wata dokar gudanar da lamura bisa tanadin Islama da ba wa mata ‘yanci hakanan da hurumin furta albarkacin baki.

Kammalawa;

Haka dai duniya za ta cigaba da zura ido a na ta kashe raunana a yankin Gaza don jinin mazauna yankin ba shi da darajar da duniya za ta girgiza. Haƙiƙa ƙaluble ne babba kan ƙasashen Larabawa su kara daga murya ko ma ba wani matakin fito na fito don muradun siyasa don dakatar da wannan yaƙi. Tuni yakin ya laƙume ran duk sanannun jagorin Hamas da su ka haɗa da Isma’il Haniyeh da Yahaya Sinwar. Can ma Lebanon Isra’ila ta kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah. Ko ma dai yaya za a yi ya na da muhimmanci ƙasashen Larabawa su jajirce aƙalla wajen dakatar da zubar da jini a yankin su. Isra’ila ita kadai don ta na samun goyon bayan aasashen yamma ba za ta iya nasara a kan su matuaar ta tabbatar a koron farko bakin su ya zama ɗaya.

By ukarofi