Dangote ya ƙaddamar da sabbin samfurin motocin Peugeot haɗin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin ƙera Motocin Peugeot na Dangote (DPAN), wanda ke ƙera kuma ya sayar da motocin Peugeot a Nijeriya, ya ƙaddamar da sabbin samfurin Peugeot na 3008 GT, motar da ta shahara a duniya kuma ta samu lambar yabo.

An samar da mata da injin turbo mai ƙarfin lita 1.6, Peugeot 3008 GT ta ƙara fito da kamfanin DPAN da ke Kaduna a ɓangaren hada-hadar kasuwanci ta zamani.

Wannan ya nuna wani muhimmin mataki na ƙudirin Dangote na bunƙasa ƙera motoci na gida da kuma inganta masana’antar ƙera motoci a Nijeriya.

Taron farko na Peugeot na samfurin 3008 a Afirka ya gudana ne a Ghana a cikin 2022.

Wannan ya nuna wani gagarumin ci gaba a nahiyar, musamman samar da sabon samfurin Peugeot na 3008 wanda ya shahara a duniya.

An gudanar da taron ne a kamfanin Tema Assembly Plant na Silɓer Star Auto, wanda ya samo asali daga haɗin gwiwa tsakanin Citroen, Peugeot, da Silɓer Star Auto wanda ya fara a cikin 2019.

Kamfanin ƙera Motocin Peugeot na Dangote (DPAN) ya fara ƙera shi ne tare da sake ƙaddamar da sabon samfurin Peugeot a Nijeriya, inda ya fara da ƙera Peugeot 301 a masana’antar ta Kaduna.

Tuni dai kamfanin ya faɗaɗa zuwa ƙera Landtrek pickup, 3008, 5008, da kuma na baya-bayan nan 508

Dangote ya shiga masana’antar ƙera motoci ta Nijeriya ne a shekarar 2016 lokacin da kamfanin tare da gwamnatin jihar Kaduna da Bankin masana’antu suka samu kaso mai tsoka a kamfanin na Peugeot.

A shekarar 2017, ya samu lasisin kamfanin na Peugeot, kuma a shekarar 2022, kamfanin Dangote (DPAN) ya fara aiki.

DPAN, haɗin gwiwa da Stellantis Group, gwamnatocin Kano da Kaduna, yana aiki ne daga Greenfield Ultima Assembly Plant da ke Kaduna, mai ƙera ababen hawa aƙalla 120 a kullum.

By ukarofi