Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tun daga ranar 29 ga Mayu, 2023, Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da ko ƙara wasu manyan haraji guda biyar, waɗanda ke yin tasiri matuƙa ga tattalin arzikin ƙasar.
Daga cikin waɗannan haraji, huɗu daga cikin ƙara su aka yi, yayin da aka ƙaddamar da sabon harajin guda ɗaya.
Waɗannan sauye-sauyen na ƙara janyo kashe maƙudan kuɗaɗe na yau da kullum na miliyoyin ‘yan Nijeriya da ke fama da matsananciyar yanayin tattalin arziki, da kuma gurgunta harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar.
Ana ci gaba da samun tsadar rayuwa, kuma ƙarfin sayen kayayyaki na raguwa, lamarin da ya sa ‘yan Nijeriya da dama suka shiga cikin damuwa.
A nan ga taƙaitaccen bayani na manyan haraji guda biyar da aka ƙara ko aka ƙirƙira a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
1. ƙarin kuɗin lantarki:
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) a ranar 3 ga Afrilu, 2024, ta sanar da amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga abokan hulɗarta da ke ƙarƙashin rukunin Band A.
Musliu Oseni, mataimakin shugaban NERC, ya ce daga ranar 3 ga Afrilu, abokan cinikin da ke ƙarƙashin wannan rukuni, waɗanda ke samun wutar lantarki na sa’o’i 20 a kullum, za su biya Naira 225 a kowace kilowatt (kW) – daga N66.
Gyaran dai shi ne rage kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke kashewa wajen tallafawa wutar lantarki.
Hukumar NERC ta ce harajin da aka amince da shi zai rage tallafin wutar lantarki na shekarar 2024 da kusan Naira Tiriliyan 1.14.
Gwamnatin tarayya ta ce tana da burin kawar da tallafin wutar lantarki a hankali.
2. ƙarin kashi 50 na kira, data da saƙon waya:
A watan Janairun 2024, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bai wa kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, Glo da sauransu damar ƙara farashinsu a karon farko tun shekarar 2013.
Hukumar NCC ta ƙayyade ƙarin zuwa kashi 50, duk da cewa kamfanonin na son ninka farashinsu.
Jim kaɗan bayan haka, Wale Edun, ministan kuɗi, ya bayyana cewa za a sake duba farashin sadarwa a kai a kai domin taimakawa masana’antu wajen shawo kan tsadar kayayyaki da hauhawar farashin kayayyaki.
Sai dai wannan shawarar ta fuskanci suka, musamman daga ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC, wadda ta kira hakan a matsayin nakasu ga jin daɗin ma’aikata.
3. Cajin amfani da ATM:
Kwanan nan ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara cajin cirar kuɗi ta Na’urar Cirar Kuci na ATM don ƙara kuɗaɗen shiga ga ɓangaren hada-hadar kuɗi.
Sabbin cajin, wanda ke nufin biyan hauhawar farashin kayayyaki da inganta ayyukan banki, za su fara aiki daga ranar 1 ga Maris.
A ƙarƙashin sabuwar manufar, ba za a caje abokan ciniki ba saboda amfani da ATM na bankinsu a rassa, manyan kantuna, ko sauran wuraren taruwar jama’a.
Duk da haka, cire N20,000 daga ATM na wani banki zai jawo cajin kuɗin N100. Idan ATM ɗin yana kan kasuwa ne ko sauran wuraren jama’a, ana iya biyan ƙarin caji har N500.
Kafin yanzu, abokan ciniki za su iya cire kuɗi sau uku kyauta kowane wata daga wasu ATM na bankuna.
4. ƙarin harajin kashi 15 na shigo kaya ta jiragen ruwa:
A karon farko cikin shekaru 32, Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), ta ƙara kuɗin harajin tashar jiragen ruwa, matakin da zai shafi masu shigo da kaya da masu fitar da kaya.
Abubakar Dantsoho, Manajin Darakta na NPA, ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin kuɗin ne don samar da sabbin hanyoyin fasaha na tashar jiragen ruwa, kamar Port Community System (PCS) da National Single Window (NSW), saboda hauhawar farashin kayayyaki.
Sai dai ƙungiyar masana’antun ta Nijeriya (MAN) ta soki wannan ƙaruwar, inda ta ce tuni ‘yan kasuwa ke kokawa da tsadar kayayyaki, da matsalar canjin kuɗaɗe da kuma ƙalubalen tattalin arziki.
5. Kwastom ta ƙara kashi 4 na harajin FOB:
A ranar 5 ga Fabrairu, Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta sanar da cewa za a riƙa biya kashi 4 kan darajar kayayyakin da ake shigowan da su daga waje ( FOB).
Sai dai ƙungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta buƙaci gwamnati da ta dakata da wannan cajin, domin ba a ba ’yan kasuwa damar su shirya ba.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya kuma yi gargadin cewa cajin zai cutar da ‘yan kasuwa da masu saye da sayarwa. Biyo bayan ƙorafin da jama’a suka yi, NCS ta dakatar da cajin kashi 4 a ranar 11 ga watan Fabrairu, saboda tattaunawa da ministan kuɗi Wale Edun.
