
Daga BELLO A. BABAJI
Manajan hada-hadar ƴan wasa a ƙasar Turkiyya, Gökhan Yağmur ya ce darajar ɗan wasan aro a ƙungiyar Galatasaray kuma ɗan Super Eagles ta Nijeriya, Victor Osimhen ta ragu duk ƙoƙarin da ya ke yi tun bayan komawara sa daga Napoli.
Osimhen ya ci ƙwallaye biyu da bada wasu biyu da aka ci acikin wasanni biyar tun da ya je ƙungiyar.
Manajan ya ce ba ƙoƙarin ɗan wasa ke sa ya ƙara daraja a Turkiyya ba, ya na mai cewa ana la’akari ne da yadda kasuwa ta ke.
Ya ce, wasannin kofin zakarun Turai da na gida da kuma sauye-sauyen kasuwa a gasar ƙasar ke da ikon ɗagawa ko karya darajar ɗan wasa.
Saboda haka ne darajar kasuwar ta shafi ƙungiyar da kuma ɗan wasan.
Sauran ƴan wasan da hakan ya shafa a ƙasar sun haɗa da; Simon Banza, Fred, Mauro Icardi, Hakim Ziyech da David Datro Fofana na ƙungiyar Göztepe.
