Darakta-Janar na NITDA ya jagoranci shirin ‘Infinite Game’ na bunƙasa ci-gaban dijital a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Darakta Janar na Hukumar Ci-gaban Fasahar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NITDA) Kashifu Inuwa ya yi kira ga ƴan Nijeriya da masu-ruwa-da-tsaki da su kalli sauyin dijital da idon basira a madadin abinda taƙaice shi na ƙaramin lokaci.

A lokacin da ya ke magana a taron Ranar Jagororin Kasuwanci karo na 13 da aka yi take da “Nigeria: From Reform to Recovery’, Daraktan ya bayyana cewa kowace nasara da aka samu a yayin sauyi aba ce za a yi amfani da ita wajen samar da ci-gaban hark-ar tattali.

Ya ce, tun daga samar da NITDA a shekarar, aƙalla ƴan Nijeriya 500,000 ne suke amfani da kwamfuta, idna a yau kimanin mutane miliyan 130 ke da damar shiga yanar gizo, kamar yadda cibiyar ƙididdaga ta bayyana.

Ya kuma ce, ta tsarin damawa da ci-gaban fasahar zamani a harkokin ƙasa zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙi duba da yadda ake samun ƙaruwar damanmakin kasuwanci da harkar tattali a fannin.

Daraktan ya ƙara da cewa, fasahar zamani da ƙirƙira a fannin ababe ne da ke ƙara bunƙasa acikin al’umma waɗanda za su bada gagarumar gudumawa ga samun nasara a harkar tattalin arziƙin ƙasa.

By Babaji