Neja: An yanke wa ƴar aikatau hukuncin kisa bisa laifin kashe malamai jami’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotu a Minna, Babban Binta Jihar Neja, ta yanke wa wata yarinya mai suna Joy Afekafe hukuncin kisa bisa kashe Dakta Funkilayo Sherifat Adefolalu, wadda babbar lakcara ce a Jami’ar Fasaha (FUT) dake Minna.

Mai Shari’a Mohammed Adishetu ta gabatar da hukuncin a ranar Laraba, bisa samun yarinyar da laifukan fashi da makami da kisa, waɗanda suna saɓa wa sashe na 221 da na 298 na kundin doka.

Ta ce, a ranar 28 ga watan Oktoban 2023 ne aka halaka Dakta Adefolau a gidanta dake Gbaiko a Minna.

Kotun ta ce, yarinyar tana aikin aikatau a gidan marigayiyar tun daga ranar 2 ga Oktoba, 2023.

A yayin zaman nata na ƙanƙanin lokaci ne Afekafe ta fara ɗauke-ɗauke na wasu kayayyakin gidan ciki har da wasu kuɗaɗen oasar waje. Bayan gano ta ne sai malamai jami’ar ta sallame ta.

Kasancewar hakan vai yi wa yarinyar daɗi ba, sai ta kitsa makirci da wasu abokanai biyu, wato DJ Wallex da DJ Smart, waɗanda a yanzu ake nemansu ruwa-a-jallo.

Afekafe ta shaida wa ƴan sanda cewa, a tare da mazan suka shirya kisan marigayar, inda suak farmaki ta tare da daddaɓa nata wuƙaƙe.

By Babaji