Rasha za ta ƙara adadin ɗaukar ƴan Nijeriya karatu kyauta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tarayyar Ƙasar Rasha ta amince da ƙara adadin bada gurbin karatu ga ɗalibai daga Nijeriya a kyauta daga guda 220 da ta saba zuwa sama a yayin da ta ke shirin cimma yarjejeniyar haɗin-gwiwa da Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa.

An samu ci-gaban ne a yayin zama da wakilan ofishin jakadancin Rasha da Ma’aikatar Al’adu a Abuja, ranar Alhamis.

Daga cikin ababen da aka tattauna akwai batun inganta matasa ta masana’antum ƙirƙira, musayar al’adu da haɗin-gwiwa ta fuskar tattali.

Da ta ke jawabi, Ministar Al’adu, Walwala da Ƙirƙirarren Tattali, Hannatu Musa Musawa ta alaƙanta yawan matasa da Nijeriya ke da shi wajen bunƙasa masana’antun ƙirƙira da al’adu.

Ta ce, za a yi amfani da damar hakan wajen warware matsalolin samar wa matasa ayyukan yi da matsin tattali, sauyin yanayi, ilimi da ƙalubalen lafiyar ƙwaƙwalwa.

A nasa jawabin, Ambasada A.L. Podelyshev, wanda shi ne jakadan Rasha ga Nijeriya, ya ce yana gayyatar Nijeriya zuwa babban taron yaɗa al’adu na ‘Kazan Fair’ da za a yi a watan Nuwamban 2025, inda ya kuma jaddada aniyarsu ta sake nazari game da yarjejeniyar haɗin kai na al’adu da aka gabatar shekaru biyu da suka gabata.

Ya bayyana cewa, akwai buƙatar samar da ci-gaban al’adu a tsakanin kasashen biyu ta hanyar gayyato ƙungiyoyin al’adun Nijeriya zuwa Rasha da tura na Rasha zuwa Nijeriya, yana mai jaddada ƙoƙarinsu na bunƙasa harkokin tattalin Nijeriya ta fasaha.

By Babaji