Boss Mustapha ya yi kuskure, Tinubu ya taimaka wa nasarar Buhari a 2015, inji Adamu Aliyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗaya daga cikin daɗaɗɗun na hannun daman tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana ƙin amincewarsa game da kalaman tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, kan matsayin Shugaba Bola Tinubu a nasarar Buhari ta 2015.

A lokacin da ya ke magana yayin ƙaddamar da wani littafi a Abuja, Boss Mustapha ya ce lallai Tinubu ba shi ne silar zaman Buhari shugaban ƙasa ba.

Ya ce, Buhari ya ci zaɓe ne bisa gudanarwa da ya samu na ƙuri’u miliyan 12, inda jam’iyyun da suka yi haɗaka suka samar da APC suka samar da ƙuri’u miliyan biyu zuwa uku kacal.

Saidai a yayin martani game da hakan a wata hira da gidan telebijin na Channels, Adamu Aliyu ya yi watsi da kalaman tsohon sakataren, yana mai cewa ba haka su ke ba.

Ya bayyana cewa, duk da cewa Buharin ya samu ƙuri’u miliyan 12 hakan bai wadar wajen samun nasararsa ba, inda sai da ya haɗa hannu da Tinubu kafim hakan ya tabbata.

Ya kuma zargi wasu daga cikin ƴan gwamnatin Buhari da ƙoƙarin sake rubuta tarihin wasu ababe da suka faru a yayin da ba sa nan, na gwagwarmayar siyasa a yayin kafa gwamnatin.

Akan haka ne ya jinjina wa Tinubu bisa gudunmuwarsa wajen zama ɗan takarar APC da Buhari ya yi da kuma hawansa mulki.

A cewarsa, Tinubu ya taimaka, sannan ya bada gudumawa ciki har da raka Buhari yawon kamfe a baki ɗaya sassan ƙasar, yana mai cewa ba ya son a samu rikici tsakanin shugabannin biyu.

By Babaji