Daraktan hukumar samar da ruwan sha a Katsina, Injiya Tingilin ya rasu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Injiniya Tukur Tingilin Malumfashi, ya rasu sakamakon mummunar hatsarin mota a tsakanin mararrabar Musawa zuwa Musawa a Alhamis da ta wuce.

Mutane da dama sun bayyana marigayi Tukur Tingilin a matsayin mutum mai kirki, mai sauƙin kai da kyakkyawar mu’amala.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya bayyana matuƙar alhini da jimaminsa kan rasuwar daraktan hukumar.

A cikin wata sanarwar ta’aziyya da babban sakataren yaɗa labarai na gwamna, Ibrahim Kaula Mohammad, ya fitar, gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar, musamman a daidai lokacin da gwamnati ke ƙara ƙaimi wajen inganta samar da tsaftataccen ruwan sha a sassa daban-daban na Katsina.

Sanarwar ta ce, “Gwamna Raɗɗa ya bayyana rasuwar a matsayin abin girgiza matuƙa, yana mai cewar jagorancin Injiniya Tingilin a matsayin daraktan hukumar ruwa ta Jihar Katsina ya kasance cike da hidima ta gaskiya ga al’umma har zuwa numfashinsa na ƙarshe,” – In ji sanarwar

“A ƙarƙashin jagorancinsa, an ƙara ƙaimi da ɗorewa wajen tabbatar da cewa tsaftataccen ruwan sha ya isa kowane gida a faɗin jihar,” Saƙon ta’aziyyar ya bayyanar.

Gwamnan ya ƙara da cewar yana miƙa ta’aziyya, tare da bada shaidar cewa marigayin ya rasu a matsayin musulmi nagari a cikin watan Ramadan mai alfarma, watan ni’ima yana mai nanata cewar hakan “na nuna kyakkyawan ƙarshe”,Inji Dikko.

Marigayi Tinjilin wanda na hannun daman gwamna Dikko Raɗɗa ne ana sa ran a yau za’ayi jana’izar a babban masallacin juma’a na garin Malumfashi.

By ukarofi