Dattawan Arewa sun nuna damuwa kan rikicin Ɗangote da BUA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana damuwarta kan rashin jituwar da ke faruwa tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, inda suka yi kira ga ‘yan siyasar da su rungumi zaman lafiya.

NEF ta kuma ce ta damu da yaƙin sunƙuru tsakanin fitattun ‘yan kasuwar Arewacin Nijeriya, Alhaji Aliko Ɗangote da Abdussamad Rabiu na kamfanin BUA.

Dattawan Arewa sun yi zargin cewa wannan faɗan yana shafar tattalin arziki da siyasar yankin.

A cewar NEF rikicin da ake fama da shi a yanzu tsakanin Aliko Ɗangote da Abdussamad Isiyaku Rabiu kan farashin siminti, da kuma rikicin kuɗi tsakanin Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara da Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, na qara ta’azzara ƙalubalen da yankin Arewa ke fuskanta a fannin tsaro da tattalin arziki.

Saboda haka, NEF ta yi kira ga shugabannin da ke da hannu a cikin rikice-rikicen da su yi taka tsantsan don amfanin yankin. “Muna kuma kira ga dukkan shugabanni da masu ruwa da tsaki a Arewa da su shiga tsakani ta hanyar gudanar da taron sulhu a tsakanin dukkan ɓangarorin.

“Ya zama wajibi musamman shugabannin Zamfara biyu, Lawal da Matawalle su kasance masu kamun kai tare da samar da haɗin kai akan matsalar rashin tsaro a jihar.

“Ƙalubalen da Zamfara ke fuskanta na buƙatar haɗin kai, kuma ta hanyar haɗa kai ne kawai za mu iya shawo kan rikice-rikicen da jihar ke fama da shi.

“Al’ummar jihar na fama da ƙalubale da dama da suka haɗa da rashin tsaro, talauci, da taɓarɓarewar tattalin arziki. A matsayinmu na shugabanni, ya zama wajibi a garemu mu sauke waɗannan nauyi da samar da makoma mai kyau ga ‘yan ƙasa,” inji shi.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Farfesa Ango Abdullahi, Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ya fitar a ranar Laraba.

Ƙungiyar Dattawan Arewa za ta ci gaba da sanya ido a kan ci gaban da aka samu, tare da fatan shugabannin za su dawo da martabar su ta hanyar yin sulhu daboda maslahar yankin.

By Editor