Daga BASHIR ISAH
Allah Ya yi wa jarumin wasan Hausa, Usman Baba Fategi da aka fi sani da Samanja, rasuwa.
Majiyarmu ta ce, Samanja ya rasu ne da safiyar wannan Lahadin a wani asibitin Kaduna bayan fama da rashin lafiya.
Duk da dai iyalan marigayin ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da rasuwar tasa, amma MANHAJA ta kalato cewa a wannan Lahadin za a yi jana’izar marigayin.
Marigayin ya bar dunya yana da shekara 81, kuma ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 14.
Samanja tsohon soja ne inda daga bisani ya kama aiki da Rediyon Tarayya a Kaduna.
