Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An fara shari’ar tsohuwar Ministar Fetur ta Nijeriya kuma tsohuwar shugabar ƙungiyar OPEC mace ta farko, Diezani Alison-Madueke, a birnin Landan na Birtaniy a ranar Litinin, inda take fuskantar tuhume-tuhumen karɓar cin hanci da rashawa da ake zargin ta aikata yayin da take kan muƙami.
Diezani mai shekaru 65 na fuskantar tuhume-tuhume biyar na karbar cin hanci da kuma ɗaya na haɗa baki domin aikata cin hanci, dukkansu suna da nasaba da lokacin da ta riƙe muƙamin Ministar Albarkatun Man Fetur tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 a mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.
Masu shigar da ƙara sun ce ta karɓi “kuɗi ko wasu alfanu” daga wasu mutane masu alaƙa da kamfanonin mai guda biyu tsakanin 2011 da 2015. Zarge-zargen sun haɗa da anfani da gidaje a Landan, gyaran su da biyan ma’aikatan da ke kula da su, sayen kayayyakin alatu, motocin haya masu direba, jirgin sama na ƙƙshin kai zuwa Nijeriya, da kuma karɓar fam dubu ɗari na Birtaniya a tsabar kuɗi.
Sauran tuhume-tuhumen na nuni da cewa an biya kuɗin makarantar danta, tare da sayen mata kayayyaki daga manyan shaguna irin su Harrods da Louis Vuitton, da kuma karin zirga-zirgar jiragen sama na ƙashin kai. Masu gabatar da ƙara sun ce waɗannan kyaututtuka sun zama cin hanci ne saboda sun shafi yadda ta gudanar da aikinta a matsayin minista.
A makon da ya gabata ta gurfana a gaban kotu a Landan domin batutuwan farko da suka shafi shirye-shiryen shari’a da zaɓen alƙalai masu yanke hukunci, yayin da ake sa ran shari’ar za ta ɗauki makonni 10 zuwa 12.
Wasu mutane biyu, Doye Agama da Olatimbo Ayinde, su ma na fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da ke da nasaba da wannan shari’a.
An kama Diezani a Landan tun a watan Oktoban 2015, kuma tana waje kan beli tun daga wancan lokaci. Ta musanta dukkan zarge-zargen da ake yi mata.
Hukumar yaƙi da manyan laifuka ta Birtaniya, NCA, ta ce a shekarar 2023 ne aka shigar da tuhume-tuhumen a hukumance, tana mai cewa ana zargin ta yi anfani da mukaminta wajen karɓar kuɗi domin bai wa wasu kwangiloli masu darajar miliyoyin fam.
A baya ma, hukumomin Amurka sun kwato kadarori da darajarsu ta kai dala miliyan 53.1 da ake alaƙanta su da zarge-zargen cin hanci da suka shafi Diezani. Waɗannan kadarori sun haɗa da gidajen alfarma a jihohin California da New York, da kuma wani jirgin ruwa na alfarma mai tsawon mita 65 mai suna Galactica Star.
An haifi Diezani a Fatakwal a shekarar 1960, ta yi karatun gine-gine a Birtaniya da Amurka kafin ta shiga aikin kamfanin Shell a Nijeriya. A harkar siyasa kuwa, ta taɓa riƙe muƙamin Ministar Sufuri, sannan Ministar Ma’adanai da ƙarafa, kafin daga bisani ta zama Ministar Albarkatun Man Fetur a 2010. A shekarar 2014 kuma ta zama mace ta farko da ta jagoranci ƙungiyar ƙasashen masu arzikin man fetur ta OPEC.
Shari’ar na jan hankalin duniya, musamman ganin matsayin da ta taɓa riƙe wa a Nijeriya da kuma a fagen makamashi na duniya, yayin da ake sa ran hukuncin kotun zai zama wani babban mataki a yaƙi da cin hanci da rashawa da ya shafi manyan jami’an gwamnati.
