Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ƙungiyoyin masu fafutukar kare haƙƙin masu saye sun gudanar da zanga-zanga a ofishin Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) da ke Legas, suna adawa da shirin fara ƙaƙaba dokar hana sayar da barasa a cikin leda.
Zanga-zangar, wadda Comrade Olufemi Lawson ya jagoranta ƙarƙashin inuwar ƙungiyar ‘Coalition for the Protection of Consumers Right’, ta biyo bayan rahotannin da ke cewa Darakta Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta sanar da fara aiwatar da matakan hana waɗannan kayayyaki.
Da yake jawabi ga masu zanga-zanga da manema labarai, Lawson ya bayyana matakin a matsayin wanda ya yi tsauri fiye da kima, mara la’akari da halin tattalin arzikin jama’a, kuma ba a yi cikakken nazari a kansa ba.
A cewarsa, wannan tsari na iya ci karo da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na rage rashin aikin yi da kuma raɗaɗin matsin rayuwa da jama’a ke ciki.
ƙungiyar ta yi zargin cewa aiwatar da dokar zai cutar da masana’antun ƙera barasa, masu rabawa, dillalai da kuma masu saye, tare da bayyana abin da ta kira rikice-rikicen tsari a cikin aikin NAFDAC.
Masu zanga-zangar sun ce yawancin barasar sachet da ke kasuwa a yanzu an gwada su kuma an yi musu rijista tare da amincewa daga hukumar, suna tambayar dalilin da ya sa yanzu ake kallon su a matsayin barazana.
Lawson ya ce matsalar shan barasa da yara kanana ke yi ba laifin kayayyakin ba ne, illa gazawar sa ido da aiwatar da doka a matakin sayarwa. Ya jaddada cewa kayayyakin suna ɗauke da gargaɗi warara cewa ba a yarda a sayar wa masu ƙasa da shekara 18 ba, don haka gazawar hana yara samun su na nuna matsala a ɓangaren sa ido.
ƙungiyar ta kuma musanta zargin cewa barasar leda na dauke da sinadarin barasa mai yawa fiye da kima, tana mai cewa kamfanonin da ke da lasisi a Nijeriya na bin ƙa’idojin da aka amince da su a duniya wajen auna ƙarfin barasa. Haka kuma ta watsar da hujjar gurɓatar muhalli, tana mai nuni da cewa ana amfani da irin wannan marufi na leda a wasu kayayyaki da dama kamar ruwan sha da sinadaran wanki.
Masu zanga-zangar sun riƙa ɗauke da alluna masu sauke da saƙonni da ke kira da a dakatar da dokar, a kare ayyukan yi da kuma rayuwar al’umma. Sun gargaɗi cewa tsaurara haramcin na iya janyo asarar dubban ayyukan yi a sarkar samar da barasa, daga ma’aikatan masana’antu zuwa masu sufuri da dillalai.
Daga cikin buƙatunsu akwai dakatar da aiwatar da dokar nan take, sake buɗe kamfanonin da aka rufe, da kuma fara tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki domin samar da mafita mai dogaro da bayanai da fahimtar juna. Sun kuma yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Dokoki ta ƙasa su shiga lamarin, suna gargaɗin cewa ƙin ɗaukar mataki na iya haifar da yaɗuwar zanga-zanga a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.
A lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an NAFDAC a ofishin Legas ba su yi jawabi kai tsaye ga masu zanga-zangar ba, kuma har yanzu hukumar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
