Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da ƙa’idoji da Dokokin Muhalli ta ƙasa (NESREA), ta bayyana cewa ana shan sama da lita biliyan 2.5 na ruwan sha na leda a Nijeriya duk shekara, adadi da ta ke cewa yana ƙara jefa ƙasar cikin matsananciyar barazanar gurɓacewar muhalli.
Daraktan Janar na NESREA, Farfesa Innocent Barikor, ne ya bayyana haka a Abuja yayin taron ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken “Circular Solutions to Plastic Pollution in Nigeria”, wato hanyoyin daƙile gurɓacewar muhalli saboda robobi da ledoji ta hanyar dabarun sake amfani da su.
A cewarsa, sama da kamfanoni 32,000 ne ke samar da ruwan leda a faɗin ƙasar, lamarin da ya taimaka wajen sauƙaƙa ƙalubalen samun ruwan sha mai tsafta ga jama’a da dama. Sai dai ya jaddada cewa wannan sauƙi ya zo ne da babban nauyi ga muhalli.
Barikor ya ce, yawan amfani da ledojin ruwan sha guda-ɗaya kacal na janyo toshe magudanan ruwa, ambaliyar ruwa a birane, lalacewar muhalli da kuma barazana ga lafiyar jama’a da namun daji.
Ya bayyana cewa sabon shirin na GEF Child Project 11193 wata babbar dama ce ga Nijeriya domin tinkarar matsalar ta fuskar da ta wuce tattara shara kawai.
A cewarsa, shirin zai mayar da hankali kan rigakafin gurɓacewar tun daga tushe, ƙirƙire-ƙirƙire, gyaran manufofi da sauye-sauyen tsarin da za su samar da ɗorewar mafita.
“Wannan shiri ya dace da manufofin muhalli na ƙasa da kuma nauyin da NESREA ke dauke da shi na kare muhalli domin amfanin al’ummomin yau da na gobe,” inji shi.
Daga ɓangaren shirin muhalli na Majalisar ɗinkin Duniya, wakiliyarsu Isabella Vanderbeck ta bayyana Nijeriya a matsayin muhimmiyar ƙasa a yunƙurin rage gurbacewar robobi a duniya. Ta ce lokaci ya yi da za a rungumi sabbin hanyoyi masu ɗorewa domin rage dogaro da robobi na amfani sau ɗaya.
Kuma, jami’a daga GEF, Evelyn Swain, ta sake jaddada goyon bayan ƙungiyarsu ga Nijeriya wajen rage amfani da ledojin ruwan sha, tare da tabbatar da cewa ana samar da tsaftataccen ruwan sha cikin sauƙi ga jama’a.
Ta ce, ana kallon Nijeriya ba kawai a matsayin mai amfana da shirin ba, har ma a matsayin ƙasa mai iya ba da darussa ga sauran ƙasashe kan yadda za a tinkari matsalar robobi.
A nata ɓangaren, Babbar Jami’ar Kimiyya ta Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli ta Tarayya, Zuliat Mohammed, ta bayyana shirinsu na haɗa kai da NESREA domin tabbatar da nasarar shirin.
Masana muhalli na ganin cewa, magance matsalar ruwan leda na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, kamfanoni da kuma jama’a, musamman wajen sauya dabi’un amfani da robobi da kuma samar da hanyoyin maye gurbinsu da kayayyaki masu lalacewa cikin sauƙi ba tare da cutar da muhalli ba.
Yayin da buƙatar ruwan sha mai tsafta ke ci gaba da ƙaruwa, ana ganin cewa daidaita wannan buƙata da kare muhalli na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Nijeriya za ta fuskanta a shekaru masu zuwa.
