EFCC ta gurfanar da bankin UBA kan zargin damfarar musayar kuɗin waje ta biliyan N4.3

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da ƙara a gaban Kotun Musamman kan Laifukan Kuɗi da ke Ikeja, inda take zargin Bankin United Bank for Africa (UBA) da wasu mutane huɗu da aikata damfara ta musayar kuɗin waje da ta kai kimanin Naira biliyan 4.3.

Sauran waɗanda ke fuskantar tuhuma a ƙarar sun haɗa da Muyiwa Akinyemi, Amangbo Stephen, kamfanin Gesos Global Serɓice da kuma Fedat Global Ltd.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Rahman Oshodi, ya ɗaga shari’ar zuwa ranar 21 ga Afrilu domin a gurfanar da waɗanda ake ƙara, bayan da babu ko ɗaya daga cikinsu a kotu a ranar Litinin da aka soma sauraron ƙarar. Haka kuma babu wani lauya da ya bayyana domin kare kowannensu.

Da aka kira ƙarar, lauyan EFCC, Temitope Banjo, ya bayyana a gaban kotu tare da nuna mamaki kan rashin zuwan waɗanda ake tuhuma. Ya shaida wa kotun cewa an riga an isar da sammaci da takardun ƙarar ga dukkan waɗanda ake zargi kamar yadda doka ta tanada.

Mai gabatar da ƙƙrar ya ƙara da cewa waɗanda ake ƙara na biyu da na uku suna da cikakken bayani kan shari’ar, amma a halin yanzu sun gudu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin gano inda suke. Ya jaddada cewa rashin zuwansu ba wai saboda ba su samu sanarwa ba ne.

“Mai Shari’a, waɗanda ake ƙara na biyu da na uku sun tsere. Har yanzu muna ƙowarin gano inda suke tare da tattara hujjoji kan inda za a same su,” inji Banjo a kotu.

Daga nan sai lauyan ya roƙi kotun ta ba su ƙarin lokaci domin su gabatar da buƙatun da suka dace a hukumance, ciki har da tabbatar da cewa an isar da sammaci ga waɗanda ake ƙara yadda ya kamata.

Bayan sauraron buƙatar masu gabatar da ƙara, Mai Shari’a Oshodi ya amince da ɗage shari’ar zuwa ranar 21 ga Afrilu domin fara gurfanar da waɗanda ake tuhuma.

Ana tuhumar mutanen da kamfanonin da laifuka guda huɗu da suka haza da haɗa baki wajen aikata laifi, sata, halasta kuɗaɗen haram, da kuma riƙe kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

A cewar takardar tuhuma, ana zargin an aikata waɗannan laifuka ne a ranakun 14 ga Satumba, 2022 da kuma 20 ga Maris, 2023 a jihar Legas.

A ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen, EFCC ta ce waɗanda ake ƙara sun karkatar tare da sace naira biliyan 4.3 mallakin kamfanin Energy Shield Petrochemical Ltd.

Haka kuma hukumar ta zarge su da haɗa baki wajen sayar da kuɗin waje sama da farashin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙayyade, sannan suka riƙe da kuma halasta ribar da aka samu daga wannan mu’amala da ake zargin ta saɓa doka.

A wani ɓangare na tuhumar, EFCC ta ce bankin UBA ya riƙe wannan kuɗi a asusunsa mai lamba NGN0991931102, lamarin da ta ce ya saɓa wa sashe na 17 na dokar kafa EFCC ta shekarar 2004.

By ukarofi