Digiri ɗan kwatano: idan ɓera na da sata… 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun a watan Disamba na shekarar 2022 lokacin da wani ɗan jarida mai suna Umar Audu, da ke aikin binciken ƙwaƙwaf a jaridar New Nigerian ta yanar gizo, ya bankaɗo wata badaƙala da ke faruwa a wasu jami’o’in Jamhuriyar Benin, inda ake cinikin ba da shaidar digiri kamar gyaɗa, wanda ba sai mutum ya je ya yi karatu a aji ba, ‘yan Nijeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu kan wannan matsalar.

Sai dai tun a wancan lokacin ba a sake jin wata magana daga Gwamnatin Nijeriya, ko Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ba, sai a cikin wannan wata na Agusta, inda muka ji cewa Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta fitar da sakamakon nata binciken, wanda a ciki ta tabbatar da zargin da wancan ɗan jarida ya bankaɗo game da wannan badaƙala ta digirin bogi da wasu jami’o’i a Jamhuriyar Benin da ƙasar Togo suke bayarwa. Yayin da ake sa ran gwamnati za ta fitar da sanarwar korar duk ma’aikatan da aka ɗauka aiki da shaidar digiri ɗan kwatano, ƙarƙashin waɗannan jami’o’i da ake zargi da hannu cikin wannan cuwa-cuwa, daga shekarar 2017 zuwa yanzu, waɗanda kuma ake ƙiyasin adadinsu ya haura 22,700.

Rahoton na Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ya fitar da sunayen wasu jami’o’i fiye da 50 da ake zargi da bayar da shaidar karatu ta bogi, kodayake daga baya an sake tantance wasu daga ciki, abin da ke nuna cewa ba duka jami’o’in ƙasashen ne aka soke takardun shaidarsu ba. A binciken da gwamnatin Nijeriya ta gudanar da haɗin gwiwar hukumomin ƙasashen biyu, an gano akwai jami’o’in da suke ɗaukar ɗalibai da karantarwa ba tare da sahalewar hukumomin ilimi na ƙasashen ba, ko kuma ba a kammala tantance su ba, wasu kuma ba a ma san da zamansu ba.

Wannan mataki na Gwamnatin Tarayya ya ɗaga hankalin iyaye da matasa da dama a Nijeriya, musamman waɗanda suka yi karatunsu a waɗannan ƙasashe, kuma suka bi dukkan ƙa’idojin da suka kamata. Aliyu Naziru Abubakar ɗalibi ne da ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Iscom da ke Jamhuriyar Benin, inda ya shafe shekaru yana karatu a can. Ya shaida min cewa, ‘Lokacin da na fara jin wannan sanarwa da gwamnatin Nijeriya ta fitar hankalina ya tashi matuƙa. Babu abinda na fara tunawa kamar lokutan da nake tashi na fita karatu cikin dare da sanyin safiya. Kowa ya san irin sanyin Kwatano, saboda ruwan da yake ƙasar. A haka za mu tashi mu hana idonmu barci, lokacin da kowa yake hutawa, mu tafi karatu duk don ganin mun yi nasara a rayuwarmu, amma daga ƙarshe a ce ya zama a banza!’

Ya ƙara da cewa, ‘Tabbas zargin da gwamnatin Nijeriya take yi akan digirin Kwatano, yana faruwa da gaske. Amma ba a iya Kwatano kaɗai ya tsaya ba har da wasu gurɓatattun jami’o’in Nijeriya. Akwai inda ake zuwa ana karɓar takardar Digiri cikin wata ɗaya ko biyu wasu jami’o’in ma ba a tantance kwasa-kwasan da suke koyarwa ba, amma haka za su ɗauki shaidar kammala Digiri su baka.’

Shi ma ɗalhatu Yero, a Jamhuriyar Benin ya yi nasa karatun digirin kuma ya ce, sam bai ji daɗin yadda ake ta yamiɗiɗi akan cewa shaidar karatun Kwatano ta bogi ce ba. Yana mai cewaa, ‘Na cika da  mamaki sosai lokacin da na ji hukuncin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka kan wannn lamari. Babban abin mamakin ma shi ne kafin mu tafi karatun nan sai da muka yi bincike kan ingancin karatun jami’ar da muke son mu je mu yi karatu ta ƙarƙashin Hukumar NUC. Kafin mu buga fasfo a matsayin masu zuwa karatun jami’a a Benin. Kuma bayan mun kammala karatun mun dawo gida, da izinin gwamnatin, suka ƙara tantance takardunmu suka tabbatar da sun bai wa jami’o’inmu lasisi, wato sun gamsu da ingancinsu. Sannan suka shirya mana wata tantancewa a matsayinmu na ɗaliban da suka yi karatu a ƙasashen waje, nan ma muka tsallake har da zuwa Hidimar ƙasa, sai yanzu kuma a zo a ce mana wai gwamnati ta haramta takardun Digirin da muka yi. Gaskiya ina ganin akwai wata manufa dai ta daban. 

Yusuf Salis Namaska shi ma dai a can Kwatano ya yi nasa karatun, kuma yanzu haka ma yana jiran tafiya aikin Hidimar ƙasa ne. Ya ce min, ‘A shekarar 2021 na kammala Digirina a Jami’ar Iscom, kuma ina shirin tafiya NYSC ne aka dakatar da mu sakamakon binciken da aka ce Gwamnatin Tarayya tana yi. Babu shakka na damu matuƙa, saboda ni na je ƙasar kuma na zauna na yi karatu na tsawon shekara 3 har sai da na kammala. Amma saboda wasu baragubin ɗalibai da suke zuwa su biya kuɗi a wasu gurɓatattun makarantu a musu komai ba tare da sun je ko ƙasar ba, mu ma yanzu ta shafe mu.

Namaska ya bayyana min jin daɗinsa da yadda daga baya aka cire sunan Jami’ar da ya yi, daga cikin jerin jami’o’in da aka haramta takardun shaidar digirinsu. 

Lallai ya kamata gwamnati ta sake nazarin wannan matsala sosai, a kuma yi hukunci a kanta cikin natsuwa da adalci, kada a cutar da wanda bai aikata laifi ba, kuma ya bi ƙa’idojin da suka kama wajen samun digirinsa. Aliyu Naziru ya ce, ‘Tabbas bai dace ba a haɗa mai laifi da marar laifi a yanke musu hukunci guda ɗaya ba. Ya kamata kowa a yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata. Ba kariya nake bai wa gurɓatattun jami’o’in Kwatano ba, hasali ma na ji daɗin hakan, domin kawo gyara za a yi.’

ɗalhatu Yero kuwa shawara ya bai wa Gwamnatin Tarayya, a ganinsa korar ma’aikata da kuma ɗalibai ba shi ne mafita ba, kawo gyara a cikin karatun shi ne abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai. ‘Gwamnati ta san duk wata hanyar da za ta kawo gyara wajen tantance ingancin karatun da dalibai suka yi da rashin ingancin makarantunsu. 

In kuma har hakan kuma ba zai samu ba to, Allah Ya sa haka shi ne mafi alkhairi a gare mu.’

Sai dai duk da haka, Yusuf Namaska ya buƙaci gwamnati ta sake duba da idanun basira. Ya ce, ‘Idan ma kuskure aka samu, muna masu kiran gwamnati da babbar murya cikin ruwan sanyi, duk da mun san cewa ba za a rasa ɓatagari ba, a ɗauki matakin da ya dace a kansu, mu bamu hana ba. Amma gaskiya a yadda aka yi yanzu kan mai uwa da wabi ɗin nan bai kamata ba. Sannan kuma, ina kira ga ‘yan’uwana abokan karatu da su guji yaɗa jita-jita, zagi da cin mutunci a wannan lokaci da muke fuskantar jarabawa. Bai kamata mu yi shiru ba, gwagwarmayar da muka jima muna yi ta tafi a banza ba. Mu ma ‘yanƙasa ne kuma masu kishin cigaban ƙasarmu.’

Idan muka lura da kyau, wannan badaƙala ta taso da batutuwa da dama da suka bankaɗo wasu kura-, kurai daga ɓangaren gwamnati da ake ganin akwai sakacinta kan duk abin da yake faruwa. Kamar abin nan ne da ake cewa, idan ɓera na da sata daddawa ma na da wari. Sakacin da gwamnati take yi da harkar ilimi ya sa abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa, ga yajin aikin malamai ga rashin tsaro, da cin hanci da rashawa, ko neman lalata da ɗalibai mata, kafin a basu makin da suka cancanta su samu.

Mista Ezekiel Taddy tsohon malamin makaranta ne a Jos, wanda kuma ya shafe tsawon shekaru yana harkar koyarwa, ya bayyana cewa, rashin bai wa ilimi muhimmanci a ƙasar nan daga ɓangaren hukumomi ya sa iyayen yara da ke da halin kai ‘ya’yansu makarantu a ƙasashen waje suke ɗaukar wannan matakin, don su samu damar yin karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Ba tare da fargabar yawan yajin aiki ko rashin kayan karatu ba.

Don haka muna jan hankalin hukumomin da abin ya shafa su ƙara zage damtse a tashi a farfaɗo da darajar ilimi, da kimar makarantun ƙasar nan, idan har ana so a hana ‘yan Nijeriya fita waje don neman ilimi, a makarantun da basu wuce sakandire a Nijeriya ba.

By ukarofi