Ya kamata a riƙa damawa da mata a harkokin shugabanci – Hussaina Abdullahi Sule

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a LAFIYA

ɗiyar gwamnan Jihar Nasarawa Hussaina Abdullahi Sule ta buƙaci a riƙa bai wa mata damar shugabancin jihar da ƙasa baki ɗaya don ba su damar bayar da tasu gudunmawar.

Hussaina Abdullhi Sule ta yi kiran ne na musamman a wajen wani babban taron bita na mata na yini guda wadda aka gudanar a babban ɗakin taro na babbar jami’ar gwamnatin jihar (NSUK) da ke birnin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar.

Taron bitar na musamman na kwana guda mai taken: Gano asalinki, wato “Discoɓery women in you, wadda ofishin daraktan cibiyar bunƙasar jinsi na fannin ɗalibai na ƙasa baki ɗaya tareda haɗin gwiwar gidauniyar Barade suka shirya suka kuma gudanar yana da manufar jawo mata waje guda ne don samun haɗin kansu sa’anan su san damarmakin su da hakokin su da baiwa na musamman da Allah yayi musu da sauran su.

Datake jawabi a waje n taron matar gwamnan jihar wace ’yar cikin gwamnan na farkon Hussaina Abdullahi Sule ta bayyana cewa ya dace matuka a cigaba da jaddada mahimmancin damawa da mata a harkokin gwamnati a kuma duka matakan jagoranci shiyasa taka yadace ta sa nata baki akoyaushe don mara wa ƙudirin baya inda ta yi kira na musamman ga shugabannin ƙasar nan a duka matakai su riƙa yin la’akari da hakan.

A cewar Hussaina Abdullahi Sule lokaci ya riga ya wuce da za a riƙa kallon mata a matsayin abu mara muhimmancin maimakon haka a riƙa girmama su tareda tabbatar ana ba su dama kamar yadda ake bai wa takwarorin su maza  a duka fannonin rayuwa.

Ta ce ba tana nufin mata suna gaza da maza ba ne amma suna kira ne a rika masu dama suma yadda yadace don suma su riƙa bai da nasu gudumawa da sauran su kasancewar acewar ta a duk lokaci da aka ilmintar da ‘ya mace an ilmirtan da al’umma baki ɗaya ne da sauran su.

Ta kuma yi amfani da damar inda ta yaba wa mata a jihar dama ƙasa baki daya dangane da ƙoƙari da suka yi a yanzu wajen neman ilimin addini dama zamani inda ta buƙace su su cigaba da hakan su kuma tabbatar suna bayyana ire-iren kyawawan baiwa da Allah yayi musu don a riƙa jawosu cikin harkokin shugabancin a ƙasa baki ɗaya.

Daganan sai ta yaba wa waɗanda suka haɗa taron inda tace tabbas shirin zai ce nesa ba kusa ba wajen ɗaukaka matsayin ’ya mace cikin al’umma akoyaushe nan gaba. 

Sauran manyan baki masu jawabi a wajen taron da suka hada da shugabar jami’ar ta jihar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da mamba mai wakiltar mazabar Nasarawa ta tsakiya a majalisar dokokin jihar Hajara Danyaro da shugaban cibiyar bai wa ɗalibai tallafi na gwamnatin jihar da dai sauran su duk sun yi kira ga shugabanni da gwamnatoti a duka matakai su tabbatar suna tafiya da mata a harkokin shugabancin don ba su damar bai da nasu gudunmawa ga cibaban al’umma.

A gudanar da abubuwa da dama a yayin taron musamman tallafin bunkasar sana’oi daban-daban da ’yar gwamnan din wato Hussaina Abdullahi Sule ta bai wa kimanin sama da ɗalibai 10 na jami’ar don inganta sana’ion nasu wadda ta bayyana cewa karamcin tayi ne maimakon ta riƙa kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bikin ranar haihuwar ta da ke zuwa kwanan nan.

By ukarofi